Gwamnonin Arewa Sun Shirya Yin Sulhu da Ƴan Bindiga? Gaskiya Ta Bayyana
- Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya bayar da tabbacin cewa gwamnonin yankin Arewa maso Yamma ba za su yi sulhu da ƴan bindiga ba
- Gwamnan wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin, ya bayar da wannan tabbacin ne wajen ƙaddamar da rundunar CPG a Zamfara
- Dikko ya bayyana cewa gwamnonin kansu a haɗe yake domin ganin sun daƙile matsalar rashin tsaro a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma sun ƙudiri aniyar ƙin amincewa da duk wani sulhu da ƴan bindiga.
Gwamnonin sun ƙuduri wannan aniyar ne yayin da jihar Zamfara ta ƙaddamar da rundunar 'Community Protection Guards' (CPG) mai ɗauke da mutum 2600, cewar rahoton Leadership.
Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma kuma gwamnan jihar Katsina, Dakta Umar Dikko Radda ne ya sanar da hakan a wajen bikin ƙaddamar da jami'an rundunar a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Babu batun sulhu da ƴan bindiga' - Radda
Radda ya ce gwamnonin sun ƙudiri aniyar yin aiki tare domin kawar da ƴan ta’adda a yankin.
Ya ƙara da cewa:
"Mun yanke shawarar yin aiki tare, duk da bambance-bambancen siyasa, don kuɓutar da jama'ar mu daga matsalar rashin tsaro."
A cewarsa, a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga, babu rarrabuwar kawuna irin su APC, PDP da NNPP, sai dai haɗin kan Arewa maso Yamma.
Ya jaddada cewa jin daɗi da ci gaban yankin su ne babban abin da ke damun shugabanni na yanzu a yankin.
Sauran gwamnonin yankin za su kafa irin rundunar
Gwamna Radda ya ci gaba da cewa, tare da ƙaddamar da rundunonin a Katsina da Zamfara, sauran jihohin Sokoto, Kebbi, Jigawa, Kano, da Kaduna za su yi koyi da su.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana jin daɗinsa bisa nasarar tantancewa da horar da jami’an tsaron da aka yi don magance matsalar rashin tsaro a jihar.
Ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a jihar tare da inganta ayyukan more rayuwa.
Gwamnoni biyar na jihohin Sokoto, Kebbi, Jigawa, Kano, Katsina, da mataimakin gwamnan jihar Kaduna suka halarci taron kaddamar da rundunar ta CPG a hukumance.
CDS Ya Aike da Sako Ga Ƴan Ta'adda a Najeriya
A baya rahoto ya zo cewa babban hafsan tsaro na ƙasa (CDS) ya aike da saƙo ga ƴan ta'adda.
Janar Musa ya roƙi ƴan Najeriya su ci gaba da taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan sirri don kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng