An Gama Biyan Bashin Daloli, Bankin CBN Ya DaukaHanyar Farfado da Kimar Naira

An Gama Biyan Bashin Daloli, Bankin CBN Ya DaukaHanyar Farfado da Kimar Naira

  • Babu wani kamfanin jirgin sama da zai yi ikirarin yana bin babban bankin Najeriya bashin daloli
  • Gwamnan CBN ya amince an batar da $64m domin a gama biyan duk wani tsohon bashi a kasuwa
  • Tun da an sauke nauyi, za a iya amfani da dalolin da aka samu nan gaba wajen farfado da kimar Naira

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN ya sanar da kammala biyan kudin kasar wajen da kamfanonin jirage su ke bin shi bashi.

Daga yanzu, The Nation ta ce babu wasu dalolin kamfanonin jiragen sama na kasashen ketare da ke hannun gwamnatin Najeriya.

CBN $.
Bankin CBN ya gagara rike Dala Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Da $64.44m da bankin CBN ya biya na karshe, an gama biyan kamfanonin jiragen bashin $136.73m da ya taru a kan wuyan kasar.

Kara karanta wannan

EFCC: Yadda aka cinye Naira Biliyan 4.6 wajen yi wa Najeriya ‘addu’a’ zamanin Jonathan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin da bankin CBN ya dauka

"Babban bankin Najeriya, ya cika alkawarin da ya dauka na sauke nauyin bashin kudin wajen kamfanonin ketare da ke kasar nan,
An kammala biyan duk wasu kudi da aka tantance da karin $64.44m ga jiragen da abin ya shafa."

- Hakama Sidi Ali

Darektar rikon kwarya ta sashen sadarwa a CBN, Hakama Sidi Ali ta tabbatar da wannan a wani jawabi da ta fitar a ranar Talata.

Hakama Sidi Ali ta ce wannan cigaba da aka samu ya nuna CBN da gaske yake yi wajen sauke nauyin da ke wuyansa a Najeriya.

The Guardian ta rahoto Darektar sadarwar ta na mai cewa Olayemi Cardoso da sauran mataimakansa su farfado da kudin gida.

Daga cikin yadda CBN zai inganta samuwar Dala akwai biyan kamfanoni hakkokinsu domin ba ‘yan kasuwa kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Dala ta lula zuwa N1400, CBN ya dauki matakin kubutar da ragowar darajar Naira

Baya ga biyan bashin, Sidi Ali ta ce suna neman yadda za a karfafi Naira a kan Dala kuma za a gyara alaka da kamfanonin jiragen.

Domin ganin an magance karyewar darajar Naira, gwamnan CBN ya fito da gyare-gyare kuma an bukaci ‘yan kasuwa su bi a hankali.

Nawa Dala ta ke a yau?

Legit tana da labarin yadda Dala ta tashi saboda karancin da ake fama da ita. A ranar Talata, an saida $1 a kan N1460 a kasuwar caji.

Wani da aka saye Dalarsa a banki, ya sanar da Legit an biya shi sama da N850 a kan $1.

Addu'o'in Naira biliyan 4.6

A lokacin da ta’addacin Boko Haram ya yi kamari, an fitar da kudi da nufin sayen makamai, ana da labari har yanzu ana kotu.

Shari’ar Amb. Bashir Yuguda da EFCC ta tona yadda kudin makamai suka shiga hannun ‘yan siyasa da kamfanoni a 2014-2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng