Abun Bakin Ciki Yayin da Almajiri da Mai Gadin Makaranta Suka Dauki Ransu a Kano
- Al'ummar jihar Kano sun fuskanci wasu abubuwan tashin hankali a baya-bayan nan sakamakon aika-aikar da wasu suka aikatawa kansu
- An samu mai gadin wata makarantar kudi da wani almajiri da suka dauki ransu a wurare mabanbanta a jihar
- Rundunar 'yan sandan jihar Kano da Mai anguwar Tudun Wada da ke jihar sun tabbatar da faruwar lamuran biyu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Nuradeen Shehu, mai gadin wata makarantar kudi a unguwar Danmusa, Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale ta jihar Kano, ya dauki ransa.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Hussaini Gumel, ya tabbatar da cewar lamarin ya afku ne a daya daga cikin ajujuwan da ke makarantar, rahoton Daily Post.
Ya bayyana cewa a safiyar Lahadi, 28 ga watan Janairu, ne wani Abdullahi Abdulsalam na Rijiyar Zaki ya kai wa 'yan sanda rahoton cewa mai gadin ya sheke kansa da igiya a daya daga cikin ajujuwan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gumel ya yi bayanin cewa wata tawagar 'yan sanda daga yankin Gwale karkashin jagorancin DPO sun je wajen sannan suka fasa kofar ajin ta bude.
An rahoto cewa jami'an tsaron sun dauki mai gadin zuwa babban asibitin Murtala inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Daga bisani aka mika gawarsa ga yan uwansa domin yi musu jana'iza.
Menene dalilin da ya sa Shehu ya sheke kansa?
An tattaro cewa Shehu ya sheke kansa ne saboda tsohuwar matarsa ta sake aure.
Kwamishinan 'yan sandan ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin.
Almajiri ya sheke kansa a Kano
Haka kuma, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutane biyu ne suka sheke kansa a Kano a baya-bayan nan..
Wani mutumi mai matsakaicin shekaru ya sheke kansa a hanyar Yahaya Gusau. Sannan an sake samun irin haka a Sauna Kawaji da Tsamiya a karamar hukumar Gezawa ta jihar.
Haka kuma, wani Almajiri mai shekaru 17 wanda aka bayyana sunansa a matsayin Idris Nasiru, ya dauki ransa a karamar hukumar Tudun Wada ta jihar Kano.
Nasiru, dalibi ne a tsangayar Malam Shuaibu da ke Tudun Wada. An gano gawarsa rataye a sama a wani kangon gini da ke yankin a ranar 22 ga watan Janairu.
Mai anguwar Tudun Wada, Alhaji Bako Alu, wanda ya tabbatar da ci gaban ya bayyana cewa ana gudanar da bincike.
'Yan sanda sun kama mutum 5 a Kano
A wani labari na daban, mun ji cewa 'yan sanda a Kano sun ce sun kama mutum biyar daga suka tada zaune tsaye bayan da Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Kano.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Malam Hussaini Gumel, ya bayyana hakan a wayar tarho da kamfanin dillancin labarin na kasa (NAN) a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng