Mai Gadin Makaranta a Kano Ya Dauki Ransa a Cikin Aji Saboda Tsohuwar Matarsa Ta Sake Aure
- Wani Nurudeen Shehu, mai shekaru 37, ya rataye kansa har lahira a ranar Lahadi a wata makaranta da ya ke aikin gadi a Kano
- An tattaro cewa, Shehu ya samu labarin tsohuwar matarsa ta yi wani sabon aure, lamarin da ya ja ya dauki wannan mumunan hukuncin
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar hakan a ranar Talata, inda kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce an yi wa matashin sutura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Wani mai gadi a kwalejin Prestige International, Nurudeen Shehu, mai shekaru 37, ya dauki rayuwarsa da kansa saboda tsohuwar matarsa ta kara wani aure a Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Shehu ya dauki ransa a cikin daya daga cikin ajujuwan kwalejin a ranar Lahadi, rahoton The Punch.
Shehu ya rataye kansa a cikin ajin makaranta
Gumel ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A ranar 28 ga watan Janairu da misalin karfe 10:30 na safe, Abdullahi Abdulsalam na Rijiyar Zaki ya ba mu rahoton cewa sun samu gawar Shehu a rataye a cikin aji.
“Yan sanda daga sashin Gwale, sun garzaya da gawar zuwa asibitin Murtala, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa, sannan aka mika gawarsa ga iyalansa don yi masa sutura."
Yan sanda za su gudanar da sahihin bincike
Tribune Online ta tattaro cewa, labarin auren tsohuwar matarsa ne ya ja Shehu ya dauki wannan mumunan hukuncin na daukar ransa da kansa.
Gumel ya yi alkawarin cewa rundunar ‘yan sandan za ta gudanar da cikakken bincike domin gano al’amuran da suka haifar da hakan.
Daliba ta dauki ranta saboda saurayi ya rabu da ita
A wani labarin kuma, wata daliba ‘yar shekara 24 mai suna Jemima Shetima-Balami, a ranar Litinin din da ta gabata, ta dauki ranta bayan saurayinta ya kawo karshen alakarsu.
An ruwaito cewa Jamima daliba ce a sashen koyon aikin jarida a kolejin kimiyya da fasaha ta Mubi da ke jihar Adamawa.
Ana dai yawan samun rahotannin mutane na daukar rayukansu da kan su a 'yan kwanakin nan.
Asali: Legit.ng