Gwamna Radɗa Ya Raba Tallafin Miliyoyin Naira Ga Mutum 35 da Aka Ceto Daga Hannun Ƴan Bindiga

Gwamna Radɗa Ya Raba Tallafin Miliyoyin Naira Ga Mutum 35 da Aka Ceto Daga Hannun Ƴan Bindiga

  • Gwamna Dikko Radda ya tallafawa mutane 35 da aka ceto daga hannun ƴan bindiga domin su farfaɗo da kasuwancinsu
  • Malam Dikko na jihar Katsina ya bai wa kowane ɗaya daga cikin mutanen tallafin N100,000 yayin da ya karɓe su daga hannun sojoji
  • Tun da fari dakarun sojin Najeriya sun ceto mutanen daga hannun masu garkuwa bayan gumurzu a dajin Dumburum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya rabawa mutane 35 da sojoji suka ceto daga hannun masu garkuwa kyautar N100,000 kowanen su.

Gwamna Raɗɗa ya raba masu wannan tallafi ne domin su samu damar sake farfaɗo da kasuwancin su na yau da kullum idan suka koma cikin danginsu.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda.
Radda Ya Bada Tallafin N3.5m Ga Wadanda Sojoji Suka ceto A Katsina Hoto: Dr. Dikko Umar Radda Ph.D
Asali: Facebook

Wasu miyagun ƴan bindiga ne suna yi garkuwa da mutanen a kauyukan Tashar Nagulle da Nahuta da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina

Kara karanta wannan

Dakarun ƴan sanda sun yi ƙazamin gamurzu da gungun ƴan bindiga, sun samu gagarumar nasara

Amma kamar yadda Channels tv ta ruwaito, dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar kwato su bayan kazamar musayar wuta da ƴan bindigan a dajin Dumburum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka ne kwamandan rundunar Brigade ta 17, Birgediya Janar O.A Fadairo, ya miƙa mutanen ga mai girma gwamna a gidan gwamnatin jihar Katsina, rahoton The Cable.

Malam Dikko ya ƙara godewa Allah SWT

Da yake karɓan waɗanda aka ceto, Gwamna Raɗɗa ya gode wa Allah SWT bisa samun nasarar ceto su ba tare da rasa rai ko ɗaya cikin jami'an tsaro ko farar hula ba.

Malam Dikko Raɗɗa ya kara jaddada cewa an samu nasarori da ci gaba sosai a yaƙin da gwamnati ke yi da ayyukan ƴan bindigan daji.

"An kashe ‘yan ta’adda da yawa a Katsina, tare da tarwatsa sansanonin su da kwato makamai da dama sakamakon hadin gwiwar jami’an tsaro."

Kara karanta wannan

Murna yayin da sojoji suka samu gagarumar nasara a jihar Katsina

Yayin da yake yabawa da kokarin sojojin da sauran jami’an tsaro, Gwamnan ya sake nanata cewa gwamnatinsa za ta yi maganin duk mai alaƙa da ƴan ta'adda a jihar.

Kalaman gwamnan na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed.

Rivers: Gwamna Fubara ya faɗi da ya shiga

A wani rahoton kuma Gwamna Fubara na jihar Ribas ya koka kan rikicin siyasar jihar wanda a cewarsa yana taɓa rayuwarsa da ta iyalansa.

Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike, sun samu saɓani kan yanayin jagoranci da jan akalar siyasar jihar mai arzikin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262