'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki a Kaduna, Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure da 'Ya'yanta
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Kidandan da ke ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna
- Miyagun ƴan bindigan a lokacin farmakin sun yi awon gaba da wata matar aure tare da ƴaƴanta uku bayan sun kutsa musu cikin gida
- Majiyoyi sun bayyana cewa mijin matar ƴan bindigan suka so sacewa sai ya yi musu turjiya wanda hakan ya sanya suka sace iyalansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun sace wata matar aure da ƴayanta uku a ƙauyen Kidandan da ke ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 12:00 na dare, inda suka riƙa harbe-harbe don tsoratar da mutanen ƙauyen.
Majiyoyi sun bayyana cewa tun farko ƴan bindigan sun shirya sace mijin matar ne amma sai ya ƙi yarda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mijin matar ya samu raunuka sakamakon turjiyar da ya yi wa ƴan bindigan, rahoton Aminiya ya tabbatar.
Ta wacce hanya ƴan bindiga suka sace su?
Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa:
"Sun yi ƙoƙarin fitar da shi daga gidan, amma ya ƙi yarda ya bi su. Sun yanke shawarar ɗaukar matarsa da ƴaƴansa uku. Daga baya an garzaya da mutumin asibiti saboda raunukan da ya samu."
Alhaji Abubakar Umar Ruka, Hakimin ƙauyen Kidandan ya tabbatar da sace mutanen, inda ya ce dukkan waɗanda aka sace mata ne.
A cewarsa, bai da tabbacin ko matar gidan da aka sace ita ce mahaifiyar yaran guda uku.
Ƴan Bindiga Sun Sace Amarya da Ango a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai sabon hari a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu ma'aurata sabon aure a ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar.
Ƴan bindigan sun sace ma'auratan ne a ƙauyen Madabanciya da ke ƙaramar hukumar ta Bungudu. Ƴan bindigan sun kuma sace dabbobi da kayayyaki masu tarin yawa a yayin harin da suka kai.
Asali: Legit.ng