An Shiga Dar-dar Bayan Mahara Sun Sace 'Yan Sanda 3 a Bakin Aiki da Ke Kare Jama'a, Bayanai Sun Fito

An Shiga Dar-dar Bayan Mahara Sun Sace 'Yan Sanda 3 a Bakin Aiki da Ke Kare Jama'a, Bayanai Sun Fito

  • An shiga tashin hankali yayin da masu garkuwa suka sace jami'an 'yan sanda guda uku a jihar Delta
  • Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi 28 ga watan Janairu a yankin Ohoror da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Edafe Bright ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi 28 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - 'Yan bindiga sun sace wasu jami'an 'yan sanda guda uku yayin da suke karbar kiran gaggawa a jihar Delta.

Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi 28 ga watan Janairu a yankin Ohoror da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar.

Kara karanta wannan

An kama 1 daga kasurguman 'yan bindigan da suka sace Nabeeha da 'yan uwanta a Abuja

Mahara sun sace jami'an 'yan sanda 3
Mahara Sun Sace 'Yan Sanda 3 a Bakin Aiki a Delta. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Yadda maharan suka yi nasarar sace 'yan sandan

TheCable ta tattaro cewa maharan sun tafi da bindigu kirar Ak-47 cike da alburusai a cikinsu na jami'an 'yan sandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sandan da aka sace na daga cikin jami'ai shida da aka tura kan hanyar Ughelli zuwa Patani don binciken ababan hawa.

Wani matashi ne mai suna Moses Progress ya kai rahoton cewa wasu makiyaya sun kwace masa waya da kudi inda aka hada shi da 'yan sandan uku.

Martanin rundunar bayan sace 'yan sandan a Delta

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Edafe Bright ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi 28 ga watan Janairu.

Bright ya ce jami'ansu suna nan su na aiki ba dare ba rana don tabbatar da dalilin bacewar tasu, cewar Chronicle.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace sufetocin yan sanda 3 tare da bindigunsu

"Tabbas an sace su, muna kokarin sanin dalilin bacewarsu da kuma neman kwato su.
"Yanzu haka an kama wani da ake zargin da hannunsa a cikin lamarin."

Wannan na zuwa ne yayin da garkuwa da mutane ke kara kamari kullum a fadin kasar baki daya.

An hallaka hadimin Akpabio

Kun ji cewa wasu matasa magoyan jamiyyar APC sun hallaka hadimin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Ana zargin shugabannin jam'iyyar da daukar nauyin matasa da suka yi wa Ime dukan kawo wuka har ya mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.