Murna Yayin da Sojoji Suka Samu Gagarumar Nasara a Jihar Katsina

Murna Yayin da Sojoji Suka Samu Gagarumar Nasara a Jihar Katsina

  • Dakarun sojoji a jihar Katsina sun samu nasarar ceto mutum 25 da ƴan ta'adda suka sace a jihar
  • Sojojin sun samu nasarar ne bayan sun dira a maɓoyar ƴan ta'addan da ke cikin daji a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar
  • Mazauna yankin sun nuna farin cikinsu tare da yaba wa sojojin kan wannan gagarumar nasarar da suka samu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Sojoji a jihar Katsina sun ceto mutum 35 da aka yi garkuwa da su daga sansanonin ƴan ta’adda da ke kusa da ƙaramar hukumar Batsari a ranar Lahadi.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa mutum 31 daga cikin waɗanda aka ceto an yi garkuwa da su ne mako guda da ya gabata a Tashar Nagulle, inda suka nemi N60m a matsayin kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Dakarun ƴan sanda sun yi ƙazamin gamurzu da gungun ƴan bindiga, sun samu gagarumar nasara

Sojoji sun ceto mutanen da aka sace a Katsina
Sojoji sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a jihar Katsina Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sauran mutum huɗun da aka ceto an yi garkuwa da su a lokuta daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna yankunan da ke yammacin Batsari sun kasance cikin farin ciki lokacin da sojoji suka fito daga dajin wanda ke haɗe da dajin Rugu.

An yi murna kan nasarar da sojojin suka samu

Shugaban ƙaramar hukumar Batsari, Yusuf Mamman - Ifo ya nuna farin cikinsa kan wannan nasarar da sojojin suka samu.

A kalamansa:

"Nasarar ta biyo bayan addu’o’i da kuma goyon bayan da gwamna ya ba mu da jami’an tsaro. A koda yaushe yana ƙarfafa mana gwiwa mu haɗa kai mu yi aiki da jami’an tsaro a irin wannan yanayi."
"Kanal ɗin nan ya yi aiki mai kyau. Za mu ci gaba da baiwa jami’an tsaro bayanan sirri."

Ɗaya daga cikin wadanda aka ceto, Maryam Nagulle, ta ce an yi garkuwa da ita tare da wasu da dama a unguwarsu mako guda da ya wuce.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Ƴan bindigan da suka sace shugaban PDP na jiha sun aiko da saƙo mai ɗaga hankali

A kalamanta:

"An kulle mu a ɗakin da suka ajiye mu sai muka ji ƙarar harbe-harbe. Ƴan ta'addan sun gudu yayin da sojoji ke ci gaba da harbe-harbe. Ba mu iya buɗe ɗakin ba saboda sun ce kada mu buɗe. Sai sojoji suka zo suka ce mu bi su."

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Sojojin da ke aikin sun ce ba za su yi magana da ƴan jarida ba.

Kakakin runduna ta 17 ta sojojin Najeriya, Oliza Ethinlaiye, bata bayar da amsar saƙon waya da aka aika mata ba.

Sojoji Sun Sheƙe Ƴan Ta'adda 10

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar sheƙe ƴan ta'adda 10 a yankin Arewa maso Yamma.

Sojojin sun ƙwato makamai da alburusai masu yawa a hannun miyagun ƴan ta'addan masu aikata ta'addanci a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng