An tsinci Gawar Wani Matashi Babu Kunne Yashe a Bola a Wata Jihar Arewa
- Mazauna yankin Nyiman Layout, kwatas din HUDCO da ke Makurdi, jihar Benue sun wayi gari da ganin wani matashi da aka jefar a bola
- An tattaro cewa an gano matashin wanda ba zai haura shekaru 20 zuwa 25 ba da kunne daya
- An daddaure hannayen mutumin ta baya da alamun an yi masa mugun duka wanda baya rasa nasaba da karo tsakanin yan kungiyar asiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Makurdi, jihar Benue - An tsinci gawar wani matashi akan bola a garin Makurdi, babban birnin jihar Benue a safiyar Lahadi, 28 ga watan Janairu.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, an gano gawar ne a kusa da unguwar lorpuu Adai, Nyiman Layout, kwatas din HUDCO, a garin Makurdi.
An tattaro cewa hannayen marigayin, wanda ake zargin ba zai wuce tsakanin shekaru 20 da 25 ba sun kasance daure ta bayansa, sannan kuma alamu sun nuna rauni kamar dai karo tsakanin yan kungiyar asiri.
Wasu da ke hanyar zuwa wajen bauta ne suka gano matashin babu kunne daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Leadership ta rahoto cewa makasan matashin sun saka gawarsa a cikin buhu kafin suka jefar da shi.
Rundunar yan sandan jihar Benue ta ce ba a kai Maya rahoton lamarin ba tukuna.
Matsafa sun yanke mazakutar ango
A wani labari na daban, wani rahoto mai daukar hankali ya bayyana yadda wasu matsafa suka yanke mazakutar wani malamin allo a unguwar Awai da ke karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.
An ruwaito cewa, matsafan sun yiwa mutumin mai suna Alaramma Salisu Mai Almajirai yankan rago tare da yi masa aika-aikar yanke mazakutarsa a hanyarsa ta dawowa daga karbo kayan cin angoncinsa.
Rufa’i Waziri, Sarkin Awai ya shaidawa Aminya cewa, mazauna yankin sun shiga tashon hankali a sadda suka tsinci gawar Alaramma a yashe.
Amarya da kawayenta sun mutu a hatsarin mota
A wani labarin, mun ji cewa wani hatsarin mota da ya auku a kusa da Lukoro a cikin garin Edati na jihar Niger, ya yi sanadiyyar mutuwar wata amarya da wasu mata biyar, da ƙanin mijinta, da wasu mutum shida.
Hatsarin wanda auku sanadiyar wucewar ganganci, ya auku ne a yammacin ranar Juma’a lokacin da motar amaryar ta yi karo da wata.
Asali: Legit.ng