Ba a Ci Ta Zama Ba, NDLEA Na Neman Sarauniyar Kyau a Najeriya Kan Babban Laifin da Ya Shafi Kwaya
- Jami’an NDLEA sun yi ram da wani wanda ake zargin ya dawo Najeriya daga kasar Brazil dauke da miyagun kwayoyi
- Ana neman sarauniyar kyau ruwa a jallo bisa zaginta da kulla harkallar safarar miyagun kwayoyi a Najeriya
- Jami’an NDLEA na ci gaba da kame wadanda ke bata sunan Najeriya da safarar miyagun kwayoyi da haramtattun kayayyaki
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Legas - Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta alanta neman tsohuwar sarauniyar kyau, Ms. Aderinoye Queen Christma ruwa a jallo bisa zargin safarar kayan maye.
Matar wacce aka fi sani da Ms. Queen Oluwadamilola Aderinoye ta shiga allon neman NDLEA ne a ranar Laraba 24 ga watan Janairu.
Legit Hausa ta samu labarin cewa, jami’an hukumar sun dura gidan matar da Lekki a jihar Legas a ranar Laraban biyo bayan samun bayanan sirri game da harkallarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacce ake zargin dai itace sarauniyar kyau ta Commonwealth Nigeria Culture a shekarun 2015/2016 kamar yadda bayanai suka bayyana.
An tattaro kayayyaki a gidanta
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana cewa, an bankado kayan maye ciki har da tabar wiwi da haramtattun magunguna a gidan matar.
Hakazalika, jami’an sun bankado wasu motoci da kayayyaki masu tsada da matar ta adana a cikin gidan.
A aikin NDLEA irin wannan, an kama wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi da ya dawo daga Brazil mai suna Udechukwu Ekene Theophilus a filin jirgin saman Murtala da ke Legas.
Yadda dalibai a Najeriya ke shan kwaya
A wani labarin, hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a jihar Kano ta yi karin haske kan cewa dalibai shida cikin 10 da ke jihar suna shan miyagun kwayoyi.
Babban Sufeton NDLEA na jihar, Jibril Ibrahim, ya bayyana cewa adadin masu shan miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai ya yi yawa kuma ana iya cewa ya haura kashi 50% cikin dari.
Sai dai da yake karin haske kan rahoton, kakakin NDLEA, Sadiq Muhammad Maigatari, ya ce alkaluman sun ta'allaka ne kan daliban da aka yi musu magani a cibiyar gyaran halaye.
Asali: Legit.ng