Yayin Da Ake Kiran Kwankwaso Zuwa APC, NNPP Ta Yi Magana Kan Hadaka da Sauran Jam’iyyu
- Ana ta yada jita-jita cewa akwai yiwuwar hadaka tsakanin jam’iyyun adawa don kwace mulki daga jam’iyyar APC
- Jam’iyyu kamar su PDP da LP da NNPP na daga cikin manya-manyan jam’iyyun da aka lissafa cewa suna shirin hadewa
- Sai dai Sakataren jam’iyyar NNPP, Oladipopo Olayokun ya karyata hakan inda ya ce babu kamshin gaskiya a maganar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Sakataren jam’iyyar NNPP, Oladipopo Olayokun ya yi martani kan jita-jitar hadewar jam’iyyar da sauran jam’iyyu.
Oladipopo ya ce ba zai iya tuna ranar da jiga-jigan jam’iyyar NNPP suka yi zama da wasu ba don yi maja a Najeriya.
Mene NNPP ke cewa kan hadaka?
Olayokun ya bayyana haka yayin hira da jaridar Punch inda ya ce jam’iyyar da Rabiu Kwankwaso ke jagoranta ba ta yi zama da wasu kan maja ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon NNPP ya ce duk da jam’iyyar ta yi hadaka da wasu bayan zaben 2023, an yi hakan ne saboda shari’ar zaben da aka karkare.
Ya ce gamayyar da suka yi a wancan lokaci kwata-kwata ba shi da alaka da zaben 2027 kamar yadda ake hasashe, cewar Daily Trust.
Ya ce:
“Duk lokacin da muka bude radiyo ko talabijin sai dai mu ji ana cewa wai NNPP ta na hadaka da wasu jam’iyyu.
“Bansan ranar da a matsayina na sakataren jam’iyyar ba da muka yi ganawa kan cewa muna yi don wata hadaka.
“Tabbas wata daya baya, akwai labarai cewa jam’iyyu shida ko bakwai sun yi hadaka amma kwata-kwata ba akan zaben 2027 ba ne.”
Ainihin dalilin hadewarsu a baya
Olayokun ya ce watakila a gaba hakan ya faru amma a yanzu shari’ar zabe ne kawai ya hada jam’iyyun kuma mungode Allah mun yi nasara, Legit ta tattaro.
Ya kara da cewa:
“Ana gama shari’ar zabe na Kotun kararraki da kuma Daukaka Kara jam’iyyun adawa sun samu labarin cewa APC na shirin kwace kujerun jihohi.
“Shiyasa muka hada kai don tabbatar da hakan bai faru ba, wannan shi ne dalilin haduwar ba akan 2027 ba ne.”
Abba ya gargadi mukarransa
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya gargadi mukarrabansa da jami’an tsaro kan mutunta jama’a.
Abba ya bayyana haka ne bayan ayarin motocinsa sun buge wata mata inda ya sauko musamman daga motarsa don ba ta hakuri.
Asali: Legit.ng