Gwamnan Arewa Ya Bayyana Abu 1 da Ya Hana a Kawo Karshen Matsalar Tsaro a Jiharsa
- Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang ya yi tsokaci kan dalilin da ya sanya aka kasa shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar
- Gwamnan ya bayyana cewa ta'ammali da miyagun ƙwayoyi na taka muhimmiyar rawa wajen rashin tsaro a jihar
- Gwamnann ya yi gargaɗin cewa duk wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi da su kwashe kayansu su bar jihar domin ba za su ci gaba da lamuntar hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Caleb Mutfwang, gwamnan jihar Plateau, ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na taka rawa wajen ƙara taɓarɓarewar matsalar rashin tsaro a jihar.
A makonnin baya-bayan nan dai an kai hare-hare da dama a jihar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutanen da bai gaza 200 ba, cewar rahoton TheCable.
A ƴan kwanakin da suka gabata, wasu ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan karamar hukumar Mangu, tare da kona mutane sama da 27 a kauyen Kwahaslalek.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Gwamna Mutfwang ya ce kan matsalar rashin tsaro?
Da yake jawabi yayin wata ziyara da ya kai ƙaramar hukumar a ranar Juma’a, Mutfwang ya ce kashe-kashen na nuni ne da shan muggan ƙwayoyi, inda ya ce dole ne a kawo ƙarshen safarar miyagun ƙwayoyi, cewar rahoton Channels tv.
A kalamansa:
"Tabbas, akwai batun amfani da ƙwayoyi, wannan wani abu ne da ya kamata mu tunkara domin samun damar magance matsalolin da ke tattare da matsalar shan miyagun ƙwayoyi a cikin al’ummarmu.
"Wannan shine dalilin da ya sa muke son yin amfani da wannan kafar don gaya wa masu sana’ar muggan ƙwayoyi su sani cewa lokacinsu a Plateau ya ƙare, ba za mu ƙara yarda da hakan ba.
"Za mu bi su, kuma idan suna da duk inda suke son yin kasuwancin su, tabbas Plateau ba wurin ba ne."
Gwamna Mutfwang Ya Sassauta Dokar Hana Fita
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sassauta dokar hana fita da ya sanya a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.
Gwamnan ya ce sassauta dokar ya biyo bayam fara daidaitar al'amuran tsaro da aka samu a ƙaramar hukumar.
Asali: Legit.ng