Hafsan Soji Ya Shiga Babbar Matsala Bayan Zarginsa da Hannu a Cin Hanci da Rashawa

Hafsan Soji Ya Shiga Babbar Matsala Bayan Zarginsa da Hannu a Cin Hanci da Rashawa

  • Bello Matawalle ya ce ma'aikatar tsaro zata gudanar da bincike kan zargin cin hanci da ake wa hafsan sojin ruwa
  • Karamin ministan tsaro ya faɗi haka ne yayin martani kan wata badakala da aka bankaɗo ana zargin hafsan rundunar
  • A cewarsa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba zata lamurci ko wane kalar rashawa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce za ta binciki zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Ma'aikatar tsaron ta ce zata gudanar da bincike kan zargin duk da cewa zarge-zargen na iya zama na yaudara da kuma rashin gaskiya, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

Bello Matawalle.
Matawalle: Zamu Binciki Hafsan Sojin Ruwa Kan Zargin Cin Hanci Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ne ya bayyana haka bayan wani zargin da aka buga a wata kafar yada labarai ta yanar gizo kan babban hafsan rundunar sojojin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki za a ɗauka kan lamarin?

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Henshaw Ogubike, ya rattaɓawa hannu a madadin ministan, ya ce:

"An ja hankalin ma’aikatar tsaro kan wani labari da jaridar People’s Gazette ta buga a kwanan nan wanda ta bankaɗo wasu zarge-zarge kan babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.
"Da yake tsokaci kan batun, karamin ministan tsaro Muhammed Bello Matawalle, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta da sassauci kan batun cin hanci da rashawa.
"Ko da yake waɗannan zarge-zargen na iya zama da ba daidai ba, ma'aikatar tsaro zata tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin rundunar sojojin Najeriya."

Kara karanta wannan

Wike ya fusata da sakacin ciyamomin Abuja a matsalar tsaro, ya musu barazana kan abu 1

Zamu gudanar da bincike mai zurfi - Matawalle

Daily Post ta ce da yake magana kan tushen da labarin ya fito, ya ce, “Muna mutunta rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana."

"Dangane da zarge-zargen, muna tabbatar wa al’umma cewa ma’aikatar tsaro za ta hada kai da hukumomin da ya dace domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin."

Gwamnan APC Ya Kori Wasu Hadimai

A wani rahoton kuma Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya ƙara korar wasu hadiman gwamnatinsa yayin da ya sa ƙafa a zangon mulkinsa na biyu

Shugaban gwamnonin APC ya kori baki ɗaya jagororin hukumar ISWAMA nan take, sannan kuma ya naɗa sabbin da zasu maye gurbin

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262