Jam'iyyar PDP ta Dau Zafi Kan Sace Shugabanta, Ta Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu
- Jam'iyyar PDP ta nuna takaicinta kan sace shugaban jam'iyyar da aka yi na jihar Legas kan hanyarsa ta dawowa daga tafiya
- Jam'iyyar PDP cikin wata sanarwa da ta fitar ta yi Allah wadai da yadda sace-sacen mutane ke ƙara ƙaruwa a ƙasar nan a mulkin Tinubu
- PDP ta buƙaci jami'an tsaro da su gaggauta ceto shugaban jam'iyyar daga hannun miyagun da suka yi garkuwa da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta buƙaci a gaggauta sakin shugaban jam'iyyar reshen jihar Legas Hon. Philip Olabode Aivoji, wanda aka sace a hanyarsa ta zuwa Legas daga Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Hakan dai na ƙunshe a wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu.
Jam'iyyar ta kuma yi Allah wadai kan yadda ake yawaitar samun sace-sacen mutane domin karɓar kuɗin fansa a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ta kuma yi kiran da a gaggauta sakin duk wasu waɗanda suke tsare a hannun masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan.
PDP ta nuna takaicinta kan yadda lamuran tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, wanda ta ce har yanzu ya gaza yin wani kataɓus a kai.
Wane saƙo PDP ta aike da shi?
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"PDP ta damu matuƙa kan lafiyar Honorabul Aivoji musamman la'akari da shekarunsa da yanayin lafiyarsa."
"Jam’iyyar PDP ta buƙaci jami’an tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don ganin an sako Honorabul Aivoji da duk wasu ƴan Najeriya da suke tsare a sansanonin masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar nan.
"Jam’iyyar mu na kira ga ƴan Najeriya da su kasance cikin shiri, su kuma ci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya a kokarinsu na kare al’ummarmu a wannan mawuyacin lokaci."
PDP Ta Yi Martani Kan Tsige Kakakin Majalisar Ogun
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun ta yi martani kan tsige kakakin majalisar dokokin jihar da ƴan majalisar suka yi.
Jam'iyyar ta bayyyana cewa matakin ya dace duba da yadda ake tuhumarsa da aikata almundahana mai tarin yawa.
Asali: Legit.ng