A Karshe, Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Nemi Afuwar Mutane Kan Kuskuren Kashe Bayin Allah a Arewa
- Shugaban sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya ziyarci jihar Nasarawa domin neman afuwa kan abun da ya faru a 2023
- Babban hafsan tsaron ya ce bam da rundunar ta sakarwa yan farar hula a garin Rukubi a Janairun 2023, ba da gangan tayi ba
- Abubakar, ya nemi zaunawa da yan uwa ko wakilan wadanda harin ya ritsa da su a kokarinsu na son rufe zancen tare da kwantar masu da hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Shugaban rundunar sojojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya nemi yafiyar gwamnatin jihar Nasarawa da iyalan wadanda suka mutu a harin bam na 2023.
A wani yayyafin bam da aka yi bisa kuskure, rundunar sojin ta sakarwa mazauna garin Rukubi da ke Doma, hedkwatar karamar hukumar Doma ta jihar bam, a watan Janairun 2023.
Babban hafsan tsaron ya bayyana cewa harin da aka kai ta sama ba da gangan ba ne, jaridar Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya fadi haka ne da yake magana a yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai wa Gwamna Abdullahi Sule a gidan gwamnati da ke garin Lafiya, babban birnin jihar a ranar Juma’a, 26 ga watan Janairu, 2024.
Abubakar ya ce rundunar sojin saman ta samu bayanan sirri cewa an hangi wasu yan ta'adda kan babura a wani wuri a kusa da garin Rukubi.
Sai dai kuma, ya bayyana cewa a kokarin rundunar na tunkarar miyagun da makamai, sai bayin Allah yan farar hula a yankin suka rasa rayukansu.
Muna so a rufe zancen - Rundunar soji ta roki gwamanan Nasarawa
Ya kuma bayyana cewa sun ziyarci jihar ne domin gwamnan ya sada su da yan uwa ko wakilan wadanda harin kuskure da kai a Rukubi ya ritsa da su.
A cewarsa, suna son tuntubar wadanda abun ya ritsa da su, yan uwa ko wakilansu kan bukatar kwantar da hankali da rufe batun.
Abubakar, wanda ya koka kan tabarbarewar tsaro a jihar, ya ba su tabbacin cewa rundunar sojin saman ta jajirce don kawo karshen annobar garkuwa da mutane, ta'addanci, fashi da makami da fashin shanu a Nasarawa da Najeriya baki daya.
Gwamna Sule ya yi martani
Da yake mayar da martani, Gwamna Sule ya mika godiya ga rundunar sojin saman kan yarda da kurakuranta da kuma yadda ta yarda za ta kwantar da hankulan wadanda abun ya ritsa da su da yan uwansu.
Gwamnan wanda ya nuna raunin zuciya a lokacin da yake magana kan lamarin, ya tuna yadda wani dan shekaru 80 ya rasa yaransa su tara da shanaye sama da 80 a lamarin, rahoton Trust Radio.
Miyetti Allah ta kara kafa dokoki
A wani labarin mun ji cewa kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) ta nemi gwamnatin Tinubu ta diyyar farar hular da sojoji suka kashe a harin bama-bamai a fadin kasar.
Shugaban kungiyar MACBAN na kasa, Baba Othman-Ngelzarma, ya gabatar da bukatar a ranar Laraba a Abuja, inda ya roki sojoji su rinka yin taka tsan-tsan yayin kai harin sama.
Asali: Legit.ng