Kano: Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Wani Matashi da Bashin Miliyan 2 Ya Sa Zai Kashe Kansa
- Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta ceci wani matashi mai suna Saifullahi Rabiu da ya yi kokarin kashe kansa ta hanyar rataya
- Hukumar ta ce Rabiu ya bar wasiyya kan cewa ya yi niyyar kashe kansa saboda bashin naira miliyan biyu da ake binsa kuma ya kasa biya
- Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a kusa da gidan Sarkin Nasarawa a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceci wani matashi dan shekara 37 wanda ya yi yunkurin rataye kansa a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu.
Matashin mai suna Saifullahi Rabiu, ya rubuta wasikar 'kashe kai', inda ya bayyana cewa ya yanke shawarar mutuwa ne saboda bashin naira miliyan biyu da ake binsa lokacin neman biza.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar da ya rabawa manema labarai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar:
"Dakin karbar korafi na hukumar ya samu kiran gaggawa misalin karfe 10:07 na safiya daga ma'aikatar ayyuka da gidaje ta jihar, kan cewar wani na kokarin kashe kansa a kusa da gidan Sarkin Nasarawa.
"Lokacin da jami'an hukumar suka isa wajen misalin karfe 10:10 na safiya, sun taras da Saifullahi Rabiu cikin mawuyacin hali."
An mika matashin ga rundunar 'yan sanda
A cikin takardar wasiyyar da Rabiu ya bari, ya bayyana cewa ya biya naira dubu 500 daga cikin kudin, amma ya gaza biyan sauran.
Ya kuma yi nuni da cewa barazana da cin fuskar da mai binsa bashin yake yi masa ne ya sa shi yanke hukuncin kashe kansa.
A cewar Abdullahi, bayan an ceci Saifullahi Rabiu, kuma an mika shi ga DPO Zaharaddini na ofishin 'yan sanda da ke Farm Centre, din ci gaba da bincike.
Kotu ta garkame tsohon dan Majalisa shekaru 5
A wani labarin, Kotun Koli ta yanke hukuncin daurin shekara biyar ga Farouk Lawan, tsohon dan Majalisar Tarayya bisa kama shi da laifin karbar cin hanci da rashawa.
An gurfanar da Lawan ne gaban Babbar Kotun Tarayya a shekarar 2021, kan karbar dala 500,000 daga hannun wani dan kasuwa don cire kamfaninsa daga tuhumar tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng