Kano: Yayin da Hisbah Ke Kokarin Kama Murja, Sheikh Rijiyar Lemo Ya Yi Magana Kan Ayyukan Hukumar

Kano: Yayin da Hisbah Ke Kokarin Kama Murja, Sheikh Rijiyar Lemo Ya Yi Magana Kan Ayyukan Hukumar

  • Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya yi magana kan ayyukan hukumar Hisbah
  • Shehin malamin ya gargadi mutane kan kushe ayyukan hukumar inda ya shawarci jama'a su musu addu'a
  • Rijiyar Lemo ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu yayin wani karatunsa da ya gabatar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya soki mutane da ke kushe ayyukan Hukumar Hisbah a Kano.

Shehin malamin ya ce ba dai-dai ba ne abin mutane ke yadawa cewa ba sa hukunci kan masu kudi sai talakawa.

Rijiyar Lemo ya magantu kan ayyukan hukumar Hisbah a Kano
Sheikh Rijiyar Lemo ya bukaci jama'a su taya Hisbah da addu'a. Hoto: Sheikh Sani, Hisbah Command.
Asali: Facebook

Mene malamin ke cewa kan Hisbah?

Rijiyar Lemo ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu yayin wani karatunsa da ya gabatar

Kara karanta wannan

Rikicin Plateau: Ahmed Musa ya yi magana mai zafi kan matsalar da ke faruwa, ya tura sako

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rijiyar Lemo ya ce wannan ba dai-dai ba ne a wurin wanda ya san shari'ar Allah inda ya ce ka yi iya abin da za ka a doka ko umarni.

Ya ce duk abin da ya fi karfinka ba a kama ka da shi inda ya ce ita barna idan har za a iya rage ta a rage hakan ma nasara ce.

Ya kuma shawarci mutane da su guji kushe ayyukan hukumar inda ya ce addu'a ya kamata a yi musu don isowa kan manyan.

Shawarar da ya bai wa jama'a kan Hisbah

Ya ce:

"Ba dai-dai ba ne abin da wasu ke yadawa cewa 'yan Hisbah sun hana kaza sun ki hana kaza su ce talakawa suke hana wa ba sa hana masu kudi ko sarauta.
"Wannan ba magana ba ce ta wanda ya san shari'ar Allah, wanda ya san shari'ar Allah cewa ta yi ka yi iya abin da za ka iya na doka ko umarni.

Kara karanta wannan

"Ba zai illata arewa ba": Jigon PDP ya magantu kan mayar da manyan ofisoshi Legas

"Abin da ake bukata a barna shi ne a kawar da ita duka idan za a iya idan kuma ba za a iya kawar da ita ba a rageta."

Shehin ya kara da cewa bai kamata ana kushe ayyukansu ba tun da su na iya kokari ya kamata a yaba musu.

Ya ce yawan laifukan yanzu sun karu idan aka kwatanta da baya, amma yanzu abin ya yi muni tun ana jin kunya har an bari, wannan shi ne matsalar sabon Allah.

Radda ya nada kwamandan Hisbah

Kun ji cewa Gwamna Dikko Radda na Katsina ya nada Ahmad Daku a matsayin shugaban Hukumar Hisbah a jihar.

Sabon Kwamnadan hukumar, Daku shi ne tsohon gwamnan jihohin Kano da Sokoto a mulkin soja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.