Yan Sanda Sun Ki Karbar Cin Hancin Naira Miliyan 1, Sun Kama Dan Bindiga a Otal Din Kaduna
- Rundunar 'yan sanda ta ce ta samu nasarar kama wani mai garkuwa da mutane a wani otal da ke yankin Tafa, jihar Kaduna
- Rundunar ta ce bayan kama shi ne ya ba DPO na ofishin su da ke Tafa cin hancin naira miliyan daya don a sake shi amma jam'i'in ya ki karba
- A yayin da aka tuhumi wanda ake zargin, ya amsa laifin garkuwa da mutane, kuma an kama shi da sama da naira miliyan biyu na kudin fansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kaduna - Wani DPO na ‘yan sanda ya ki amincewa da karbar cin hancin naira miliyan daya da wani dan bindiga ya ba shi bayan an kama shi a wani otal da ke garin Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa dan fashin da aka kama ya bayar da cin hancin daga cikin kudin fansa da ‘yan sanda suka kwato daga hannunsa a wani otal da ke unguwar Tafa.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ASP Mansir Hassan, a ranar Alhamis, an kama mutumin ne a ranar 19 ga watan Janairu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A Daily Trust, hedikwatar sashen rundunar ta samu sahihin bayanai game da zaman wanda ake zargin a otal din st Easyway a yankin Tafa.
Bello Muhammad ya amsa cewa shi dan bindiga ne
Ya bayyana cewa jami’ansu karkashin jagorancin DPOn yankin Tafa, sun kai farmaki otal din, inda suka kama dan bindigar mai suna Bello Muhammad daga jihar Zamfara tare da kwato kudi naira 2,350,000, wadanda ake zargin na satar mutane ne.
Ya ce a lokacin da ake gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amince cewa shi mai garkuwa da mutane ne da ke gudanar da ayyukan sa a dajin Kagarko a Kaduna.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, CP A.D Ali, yayin da yake yaba wa Jami’an Tafa Dibision, ya bukaci su kara kaimi har sai an rage yawan laifuka da kama masu aika laifukan a jihar.
Asali: Legit.ng