Karyar Yan Bindiga Ta Kare: Wike Ya Dauki Muhimmin Mataki Don Kawo Karshen Rashin Tsaro a Abuja
- Ministan babban birnin tarayya Abuja ya buƙaci samun haɗin kai daga wajen sarakunan da shugabannin ƙananan hukumomi a Abuja
- Nyesom Wike ya buƙaci samun haɗin kan ne domin magance matsalar rashin tsaro da ta addabi birnin
- Wike ya kuma umarcesu da su kafa rundunar ƴan banga wacce za ta taimakawa jami'an tsaro a birnin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin kananan hukumomi da su taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro a babban birnin.
Mista Wike ya yi wannan kiran ne a wata ganawa da ya yi da sarakunan gargajiya na Abuja da kuma shugabannin ƙananan hukumomi a ranar Laraba a Abuja, cewar rahoton Premium Times.
An kira taron ne domin tattauna matsalolin tsaro da birnin ke fuskanta da kuma ƙoƙarin da gwamnati ke yi na shawo kansu, rahoton TheCable ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada cewa sarakunan gargajiya da shugabannin ƙananan hukumomin na da muhimmiyar rawar da za su taka, wajen tabbatar da tsaro a yankinsu ta hanyar samar da sahihin bayanai ga jami’an tsaro.
A kalamansa:
"Sarakunan gargajiya suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da tsaron yankinsu. Kun san mutanen da ke yankinku. Idan akwai baƙin fuskokin da kuke ganin ba ku yarda da su ba, kuna da ikon kai rahoto a kansu.
"Za ku iya kiran shugaban ƙaramar hukuma don kai rahoto ga jami'an tsaro ko ofoshina domin a ɗauki mataki."
Wane umurni Wike ya ba da?
Wike ya umurci shugabannin ƙananan hukumomi shida da ke babban birnin tarayya Abuja da su kafa rundunar ƴan banga don tallafawa ƙoƙarin jami’an tsaro.
Ya buƙaci masu riƙe da sarautun gargajiya da su tabbatar da cewa mutanen da suka dace, waɗanda ba su da tarihin aikata laifuka kawai aka shigar da su a cikin ƴan bangan.
'Ana Zuzuta Rashin Tsaro a Abuja' - Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan baɓɓan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi nuni da cewa akwai masu zuzuta wutar matsalar rashin tsaro a Abuja.
Wike ya bayyana cewa masu aikata hakan ɗaukar nauyinsu aka yi domin yi wa gwamnati baƙin fenti.
Asali: Legit.ng