'Ni Dan Fashi Ne Ba Mai Garkuwa da Mutane Ba', Inji Gawurtaccen Mai Garkuwa da Mutane a Abuja

'Ni Dan Fashi Ne Ba Mai Garkuwa da Mutane Ba', Inji Gawurtaccen Mai Garkuwa da Mutane a Abuja

  • Wani da ake zargin fitaccen mai laifi ne a Abuja, Chinaza Philip-Okoye, ya musanta cewa shi ne mai garkuwa da mutane ne
  • Philip-Okoye ya ce shi ba mai garkuwa da mutane ba ne, ɗan fashi da makami ne da ke satar motoci a kan titi
  • Ya ce jami’an ƴan sandan sun kama shi ne a jihar Kaduna a kan hanyarsu ta zuwa Kano bayan sun ƙwace wata mota

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani da ake zargin fitaccen mai laifi ne a Abuja, Chinaza Philip-Okoye, ya ce shi ba mai garkuwa da mutane ba ne.

Philip-Okoye ya yi iƙirarin cewa shi ɗan fashi ne kawai yayin da yake ba da labarin yadda ƴan sanda suka kama shi, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan fashewar wani abu a Abuja, ya tafka mummunar ɓarna

Mai garkuwa da mutane ya ce shi dan fashi ne
Chinaza ya ce shi dan fashi ne ba mai garkuwa da mutane ba Hoto: @FCT_PoliceNG
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin da rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, ta tasa ƙeyar waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a birnin, a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chinaza ya musanta laifin da ake zarginsa da shi

A kalamansa:

"Ina so in bayyana cewa ni ba mai garkuwa da mutane ba ne, ni ba mai garkuwa da mutane ba ne. Sai da daddare muke sintiri, muna ƙwacen motoci, mukan kai su Kano don sayarwa.
"A wannan daren, manufarmu ita ce mu yi wa mutumin fashi, mu tafi da motarsa, amma na yi mamaki bayan da muka ƙwace motarsa, Yellow wanda yake kamar shugabanmu ya ce mutumin ya shiga bayan motar.
"Ban san dalilin da ya sa ya yi haka ba, kuma ba zan iya yin gardama da shi ba, don haka muna tafiya zuwa Kano kafin nan ƴan sanda suka ritsa mu a Kaduna inda aka cafke ni.”

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya damfari mabiyansa $1.3m, ya bayyana wanda ya ba shi umarnin yin hakan

Ƴan Sanda Sun Cafke Mai Garkuwa da Mutane a Abuja

A baya rahoto ya zo cewa rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da cafke wani fitaccen mai garkuwa da mutane a Abuja, Phillip-Okoye.

Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun kama Chinaza a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, 2024.

Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce wanda ake zargin yana hannun ƴan sanda a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng