An Shiga Jimami Bayan Tsohon Kakakin Majalisa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya da Shekaru 61
- An shiga jimami bayan rasuwar tsohon kakakin Majalisar jihar Anambra, Anayo Nnebe a Awka da ke jihar
- Marigayin ya rasu a daren jiya Talata 23 ga watan Janairu a asibitin koyarwa na Nnamdi Azikwe da ke Awka
- Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da cewa Nnebe ya rasu ne bayan ya sha fama da gajeruwar jinya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Anambra – Tsohon kakakin Majalisar jihar Anambra, Anayo Nnebe ya riga mu gidan gaskiya.
Anayo ya rasu ne a daren jiya Talata 23 ga watan Janairu ya na da shekaru 61 a asibitin Nnamdi Azikwe, cewar Vanguard.
Yaushe marigayin ya rasu a Anambra?
Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da cewa Nnebe ya rasu ne bayan ya sha fama da gajeruwar jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin wanda aka fi sani da Ichele Awka ya rike ragamar shugabancin Majalisar jihar Anambra daga 2007 zuwa 2011.
An haifi marigayin a shekarar 1963 a karamar hukumar Awka ta Kudu da ke jihar Anambra, cewar Tribune.
A shekarar 2015 an zabe shi a jam’iyyar PDP a matsayin dan Majalisa mai wakiltar Awka ta Kudu da Arewa a Majalisar.
Marigayin ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APGA
A watan Afrilun shekarar 2018, Nnebe ya bayyana aniyarsa ta sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APGA.
Kun ji cewa Dele Oni, gogaggen dan jarida, mai yada labarai a sashen Yarbanci na gidan talabijin na Najeriya (NTA), ya riga mu gidan gaskiya.
Dele Oni ya yi fice sosai a tashar NTA Channel 7 da Channel 10 a cikin shekarun 1980s zuwa 1990s.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Oni ya rasu ne a ranar Litinin 5 ga watan Yunin shekarar 2023 ya na da shekaru 73 a duniya.
Farfesa Okoro ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, Fitaccen marubuci kuma malami, Farfesa Okoro Anezionwu ya riga mu gidan gaskiya a jihar Enugu.
Dan marigayin, Chukwuma Anezionwu shi ya tabbatar da hakan a ranar Asabar 20 ga watan Janairu a jihar Enugu.
Chukwuma ya ce mahaifin nasu wanda ya wallafa sanannun littattafai da dama ya rasu ne ya na da shekaru 94 a duniya.
Asali: Legit.ng