Ta Sake Fashewa Yayin da Tsohon Gwamna Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Wawure N4bn, EFCC Ta Magantu
- Yayin da hukumar EFCC ke ci gaba da tuhumar 'yan siyasa, tsohon gwamnan Anambra ya iso kotu
- Willie Obiano ya iso Babbar Kotun Tarayyar ce a yau Laraba 24 ga watan Janairu kan wasu zarge-zarge na kudade
- Obiano ya iso kotun ne da rakiyar wasu jami'an hukumar EFCC wadanda ke zargin ya karkatar da naira biliyan 4
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya isa Babbar Kotun Tarayya kan zargin karkatar da kudade.
Obiano ya iso kotun ne tare da rakiyar wasu jami'an hukumar EFCC kan zargin badakalar naira biliyan 4, cewar Punch.
Wane zargi Hukumar EFCC ke yi kan Obiano?
Ana zargin tsohon gwamnan da karkatar da kudaden lokacin da ya ke kan mulki a jihar kafin mika mulki ga Charles Soludo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, hukumar EFCC na tuhumar tsohon gwamnan kan wasu zarge-zarge guda tara daga shekarar 2014 zuwa 2022.
Tsohon gwamnan mai shekaru 68 an gurfanar da shi ne a gaban Mai Shari'a, Inyang Ekwo a yau Laraba 24 ga watan Janairu.
Wane martani Obiano ya yi kan tuhume-tuhumen?
Sai dai bayan karanto tuhume-tuhumen da ake masa, Obiano ya musanta aikata ko da laifi daya a cikin taran, cewar Channels TV.
Lauyan hukumar EFCC, Sylvanus Tahir ya bukaci kotun ta ci gaba da tsare shi a hannun hukumar ta yaki da cin hanci.
A yanzu haka dai hukumar ta bai wa Obiano beli da sharadin gabatar da masu tsaya masa, Tribune ta tattaro.
Daga cikinsu kuwa dole akwai daraktoci guda biyu a aikin gwamnati wandanda suka mallaki filaye a Abuja.
EFCC ta gurfanar da Obiano a gaban kotu
A wani labarin, Hukumar yaki da cin hanci (EFCC) za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.
EFCC za ta gurfanar da Obiano a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Hukumar na zargin tsohon gwamnan da almundahanar kudi har naira biliyan hudu lokacin da ya ke mulkin jiha Anambra.
Asali: Legit.ng