Kisan Ummita: Kotu Ta Tsayar da Ranar da Dan China Zai San Makomarsa

Kisan Ummita: Kotu Ta Tsayar da Ranar da Dan China Zai San Makomarsa

  • Wata babbar kotu a Kano ta saka ranar karshe don yanke hukunci kan dan China, Mr Geng da ake zargin ya kashe Ummukulsum a gidansu
  • A ranar 16 ga watan Satumba, 2022 ne aka yi zargin Mr Geng ya kashe budurwarsa Ummukulsum, amma ya musanya hakan
  • A zaman da kotun ta yi, Mai shari'a Sanusi Ado-Ma'aji ya dage karar zuwa ranar 29 ga watan Maris domin yanke hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Wata babbar kotu a Kano ta dage shari’ar Frank Geng Quangrong, dan kasar China da ake zargi da kashe budurwarsa ‘yar Najeriya, Ummukulsum Sani, ‘yar shekara 22.

Wanda ake tuhumar wanda kuma ya ke zaune a rukunin gidajen 'Railway Quarters' Kano, ana tuhumarsa da laifin kisan kai.

Kara karanta wannan

Ya ci kudin banki: Kotu ta daure wani dan jihar Bauchi shekara 3 a gidan yari, an samu bayani

Dan China da ake zargin ya kashe Ummita
Kano: Dan China da ake zargin ya kashe Ummita zai san makomarsa a watan Maris. Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin, rahoton Legit Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyi sun gabatar da jawabin karshe kan shari'ar

Mai shari’a Sanusi Ado-Ma’aji, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Maris domin yanke hukunci, Daily Nigerian ta ruwaito.

Dage zaman ya biyo bayan amincewa da rubutaccen jawabi na karshe da lauyoyin masu gabatar da kara da masu kare kara Muhammad Dan’azumi da Aisha Mahmoud suka yi.

Ku tuna cewa mai gabatar da kara ya rufe jawabin karar da ake tuhumar Geng bayan da ya gabatar da shaidu shida a ranar 21 ga Disamba, 2022.

Haka kuma lauyar wanda ake kara ta rufe jawabin nata da shaidu guda biyu da suka hada da likitan mata, Dakta Abdullahi Abubakar.

Dokar da ake zargin Mr Geng ya karya

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka basarake, sun yi garkuwa da iyalansa da wasu mutane 16 a jihar arewa

A cikin shaidarsa wanda ake zargin ya shaida wa kotu cewa marigayiya Ummukulsum ta kai masa hari da wuka.

Ana zargin Geng ya daba wa marigayiyar wuka a gidanta da ke Janbulo Quarters Kano a ranar 16 ga Satumba, 2022.

Shafin Justice Watch ya ruwaito mai gabatar da karar, ya shaidawa kotun cewa laifin da ake tuhumar Geng ya saba wa tanadin sashe na 221(b) na dokar Penal Code.

An kama matashin da ke kai wa 'yan bindiga harsashi a Zamfara

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sandan Tudun Wada Zariya, jihar Kaduna sun kama wani matashi, Mansir Hassan dauke da jaka cike da alburusai a hanyar zuwa Zamfara.

Bayan tuhumarsa, Mansir ya tabbatar da cewa yana hanyar kai alburusan ga wani dan bindiga a dajin Zurmi, jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.