Gwamnan Jihar Katsina Ya Ba Jami'an Gwamnatinsa Sabon Umarni Kan Abu 1
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya umarci dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da ma'aikatan gwamnati su bayyana kadarorinsu
- Gwamnan ya yi nuni da cewa yin hakan yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da gaskiya wajen gudanar da ayyukan gwamnati
- Dikko ya bayar da wannan umarnin ne lokacin da ya karɓi baƙuncin muƙaddashin shugaban hukumar ɗa'ar ma'aikata ta ƙasa (CCB)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayar da umarnin cewa duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ma'aikatan gwamnati a jihar Katsina su bayyana kadarorinsu ga hukumar CCB.
Gwamna Radda ya jaddada cewa hakan yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da gaskiya, cewar rahoton Vanguard.
Ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Barr. Murtala Aliyu Kankia, muƙaddashin shugaban hukumar ɗa’ar ma’aikata ta CCB, a fadar gwamnatin jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake karɓar baƙuncin shugaban hukumar ta CCB, Gwamna Radda ya jaddada ƙudirinsa na samar da kyakkyawan yanayin aiki ga ma’aikatan hukumar a Katsina.
A cewarsa, akwai buƙatar jami’an gwamnati su fara bayyana kadarorinsu ga hukumar CCB, idan har suna da sha’awar yin aikin gwamnati.
Wacce rawa hukumar CCB ke takawa?
A cikin jawabinsa, Barr. Aliyu Kankia ya bayyana cewa hukumar ba kawai tana taka rawa ba ne wajen bayyana kadarori, har ma da tabbatar da bin ƙa’idojin ɗa’ar aiki ga jami’an gwamnati, rahoton Arise tv ya tabbatar.
Kankia ya yi gargaɗin cewa jami’an da ke boye kadarori ba tare da bayyana su yadda ya dace ba, gwamnatin tarayya za ta ƙwace su.
Ya kuma bayyana cewa hukuncin da za a yankewa waɗanda suka bayyana kadarorin ƙarya, sun haɗa da dakatar da su daga riƙe muƙami na tsawon shekara 10 ko rasa muƙamin da su ke kai a yanzu.
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mai sharhi kan al'amura, Zahraddeen Hamisu, wanda ya yaba da wannan umarnin da gwamnan ya bayar.
Ya bayyana cewa matakin zai ƙara sanya gaskiya da riƙon amana tsakanin masu riƙe da muƙamai na siyasa da ofisoshi na gwamnati.
Ya yi nuni da cewa matakin kuma zai daƙile yawan satar da ake samu tsakanin masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Gwamna Radda Ya Tallafawa Manoma
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gwangwaje manoman rani a jihar.
Gwamnan ya ƙaddamar da shirin ba manoman rani 2,040 kayayyakin noma kyauta domin bunƙasa harkar noma a jihar.
Asali: Legit.ng