Wayyo: Ana Mani Barazana Saboda Tona Asirin Masu Taimakon ‘Yan Ta’adda Inji Minista
- Ministan ma'adanai ya ballo ruwa tun da ya tona asirin masu hannu wajen hakar ma’adanai ta bayan fage
- Dele Alake ya tabbatar da barazanar da yake fuskanta tun da ya je gaban majalisa, ya tona asirin manya
- Mai girma Ministan ya sha alwashin magance satar ma’adanan Najeriya da wasu marasa kishi suke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ministan harkokin ma’adanan kasa, Dele Alake ya tabbatar da cewa yana fuskantar barazana saboda kalaman da ya yi.
Kwanan nan aka ji Mai girma Ministan ya fito yana zargin manya da hannu wajen hura wutar ta’addanci, Legit ta fitar da rahoton nan.
A labarin da muka samu a Punch, Dele Alake yace yana ganin barazana dalilin tona asirin masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya tabbatar da cewa ana turo masa sakonnin da ke yin barazana ga rayuwarsa game da yunkurin tona asirin masu barna.
Bodija: Minista Alake ya ziyarci Ibadan
Alake ya yi wannan tonon silili ne da ya ziyarci inda aka samu fashewar wani abu a garin Ibadan da ke jihar Oyo a farkon makon nan.
Wannnan mummunan lamari da ya auku a Bodija ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla biyar sannan akwai mutane 77 da ke jinya.
Bugu da kari, fashewar wannan abin ya yi wa gidaje kusan 60 barna a garin na Ibadan.
Alake yace tun da ya je majalisar tarayya, ya fallasa abin da ake yi wajen hako ma’adanai, ake turo masa sakonni na barazana iri-iri.
Minista yace babu babba babu yaro
Tribune ta rahoto Alake yana cewa wannan danyen aiki bai takaita da mala’u ba, kuma suna kokarin gyara harkar ma’adanai a kasar.
Duk da wadannan barazana da ministan yake fuskanta, yace ba zai saduda ba domin kuwa ba wani sabon lamari ya fadawa 'yan Najeriya ba.
"Na fada a fili, shakka babu, ina fuskantar barazana, amma wannan ba zai sa mu ja da baya ba, dole a fadi wannan abin."
"Mutane da yawa suna ta fada, ni dai kurum nayi magana da hatimin gwamnati ne, la’akari da bayanan sirri da muke samu."
- Dele Alake
ACF ta maida raddi ga Ministan jirage & CBN
ACF ta ce maida hedikwatar FAAN da wasu ofisoshin CBN Legas zai jawo Abuja ta zama kango kamar yadda Olusegun Obasanjo ya yi.
Rahoto ya zo cewa Dattawan Arewa suna zargin akwai take-taken nakasa mutanen yankinta a shirye-shiryen gwamnatin tarayyar nan.
Asali: Legit.ng