Wike Ya Bayyana Masu Zuzuta Wutar Matsalar Rashin Tsaro a Abuja
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce babu inda ba a aikata laifi a faɗin duniya nan
- Wike ya ce wasu ƴan siyasa ne ke da alhakin haifar da tashin hankalin da bai kamata ba a Abuja game da satar ƴan tsirarun mutane
- Ya ce ƴan siyasar masu ɓata suna ne, waɗanda aka ba su kuɗi su riƙa yaɗa farfaganda don ganin gwamnati ta gaza
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce wasu ƴan siyasa ne ke haddasa tashe-tashen hankula a babban birnin ƙasar.
Wike ya ce ana biyan masu ɓata sunan ne don aiwatar da farfaganda da kuma haifar da tashin hankali game da batun sace mutane.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Wike ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo wanda yanzu an goge shi wanda tashar Symfoni News ta sanya a shafinta na YouTube.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Wike ya ce kan rashin tsaro a Abuja?
A kalamansa:
"Wasu ƴan siyasa sun duƙufa wajen ganin gwamnati ba ta kai labari ba. Ta yaya ake yin hakan? Ta hanyar haifar da tashin hankali ba gaira ba dalili, da yin farfaganda idan wani abu ya faru a nan, sai su gaya muku cewa ya faru sau 25. Dole ne ku fahimci yadda tsarin mu ke aiki. Su ne ƴan ɓata suna, waɗanda ake biya."
Ya ƙara da cewa:
"Ba za a iya dakatar da aikata laifuka gabaɗaya ba. Bari wani ya gaya mani a matsayina na ƙwararre cewa akwai wani waje a duniya inda ba a aikata laifi. Domin a daren jiya anyi garkuwa da mutane a wuri ɗaya ko biyu, don haka akwai rashin tsaro a fadin birnin tarayya Abuja. Hakan ba daidai ba ne."
Majalisa Za Ta Gayyaci Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan babban birnin tarayya Abuja, Ireti Kingibe, ta bayyana cewa majalisar dattawa za ta gayyaci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Sanatan ta bayyana cewa majalisar za ta gayyaci ministan ne kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a birnin.
Asali: Legit.ng