Mahara Sun Shiga Jami'ar BUK Kano Sun Yi Garkuwa da Ɗalibai? Gaskiya Ta Bayyana
- Jami'ar Bayero da ke Kano ta musanta rahoton kai harin garkuwa da mutane a harabar makarantar
- A wata sanarwa da mataimakin rijistara ya fitar, ya ce rahoton wanda wasu ke yaɗawa ƙarya ce kuma mara tushe ballantana makama
- Ya ce ba a taɓa samun bazarana mai kama da irin wannan ba a BUK kuma ya roki al'umma su yi fatali da rahoton na kanzon kurege
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Hukumar gudanarwa ta jami'ar Bayero da ke Kano wacce aka fi sani da BUK ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa an kai harin garkuwa jami'ar.
Jami'ar BUK ta yi watsi da rahoton da ake yaɗawa na sace ɗaliban makarantar wanda ta bayyana a matsayin rahoton karya, mara tushe da aka kirkira da mugun nufi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakin rijistara mai kula da sashin hulɗa da jama'a na BUK, Lamara Garba, ya fitar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene gaskiya kan rahoton garkuwa a BUK?
Ya ce jami’ar BUK ba ta taba fuskantar irin wannan barazana ta harin garkuwa ba, yana mai karawa da cewa wadanda ke yada rahoton ba su da tunani da sanin ya kamata.
A rahoton Daily Post, Sanarwan ta bayyana cewa:
"An jawo hankalin hukumar jami'ar Bayero da ke Kano (BUK) kan wani rahoton ƙarya na yin garkuwa da wasu a harabar makarantar.
"Muna tabbatar wa al'umma cewa ba a taba samun kes ɗin yin garkuwa da mutane a cikin harabar jami’ar ba ko kadan. BUK ta jima tana ɗaukar matakan kare ma'aikata da ɗaliban jami'ar.
"Mun shiga damuwa matuƙa bisa yadda wasu marasa tunani suka kirkiri labaran karya da sanin cewa hakan zai haifar da firgici ba wai a cikin jami'a kadai ba, har da baki ɗaya birnin Kano da kewayenta."
Ya kuma yi kira ga ɗaukacin al'umma da su yi watsi da rahoton na ƙanzon kurege, yana mai ba da tabbacin cewa “Jami’ar Bayero na cikin zaman lafiya da tsaro.”
Yan sanda sun ɗauki mataki a jihar Filato
A wani rahoton kun ji cewa Dakarun ƴan sanda sun mamaye majalisar dokokin jihar Filato yayin da korarrun ƴan majalisar PDP ke shirin haddasa matsala.
Wata majiya daga cikin jami'an tsaron ta ce an ba su umarnin bincikar duk wanda zai shiga majalisar domin daƙile masu shirin tayar da yamutsi.
Asali: Legit.ng