Jibrin Dan Sudan: Mai Daukan Buhari Hoto Ya Magantu Kan Zargin Sauya Tsohon Shugaban Kasar
- An wargaza rade-radin da ake yi na cewa an sauya tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da wani
- Bayo Omoboriowo, mai daukar hoton tsohon shugaban kasar ne ya yi watsi da wannan rade-radin yayin da ya bayyana a wani shirin kai tsaye da safiya
- Ya bayyana cewa Buhari mutum ne mai alheri, kuma idan aka samu sauye-sauye a tattare da shi, shi ne zai fara gane su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Bayo Omoboriowo, tsohon mai daukar hoton tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi watsi da dadden jita-jitan cewa tsohon ubangidansa ya sauya zuwa Jibrin na kasar Sudan.
Ya yi watsi da rade-radin ne wanda ake ta yi tun a lokacin da Buhari ya yi ta fama da rashin lafiya da tsawaita zamansa a kasar Ingila a shekarar 2017.
A yayin da ya bayyana a wani shirin safiya na Channels TV, Omoboriowo mai shekaru 36 a duniya ya ce babu wani banbanci tsakanin rashin lafiyar Buhari a shekarar 2017 da kuma farfadowarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jadadda cewar Buhari ya samu sauki zuwa dan lokaci, inda tsohon shugaban kasar ya kara karfi sannan fatarsa ta murje yayin da yake murmurewa.
Omoboriowo ya warware cece-kuce kan kasancewar Buhari biyu
Buhari, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban kasa daga Mayun 2015 zuwa Mayun 2023, ya fada halin rashin lafiya a 2017 sannan aka dauke shi zuwa Ingila a farkon Mayun wannan shekarar.
Ya dawo a watan Agusta bayan ya samu kulawar likitoci.
A lokacin da yake kasar waje na tsawon lokaci, an yi yada jita-jitan cewa Buhari ya mutu sannan cewa an sauya shi da wani mai suna Jibrin daga kasar Sudan.
Nnamdi Kano, shugaban yan awaren IPOM shine ya fara yayata wannan ikirarin.
Buhari, wanda tsohon shugaban kasa ne na mulkin soja tsakanin Disamba 1983 zuwa Agusta 1985, ya karyata wadannan hasashe.
Omoboriowo, mai daukar hoton Buhari na tsawon shekaru takwas shima ya yi watsi da wannan batu game da tsohon ubangidan nasa.
Channels TV ta nakalto yana cewa:
"Zan fadi, babu wanda zan ba hakuri. A ganina, Shugaban kasa Buhari mutum ne mai alkhairi.
"Na yi irin wannan tattaunawar da wata dattijuwa a lokacin hutun Kirsimeti. Ta kai ni kicin dinta sannan ta tambaye ni, 'da gaske shi din Buhari ne?' Sai na yi kokarin yi mata bayani. Misali, nine mai daukar hotonsa, idan ya canja, ya kamata na sani.
"A ganina, ya fi kama da bayar da labarin wani mutum a lokacin da ya tafi da lokacin da ya dawo, shi din ne dai. Ya rame sannan ya murmure.
"Tattaunawar tamu dai daya ce. Lokacin da ya bai gan ni ba, ya tambaya, 'ina Bayo?' Don haka, idan ba shi din bane, ya zai san sunan mai daukar hotonsa.?"
Omobioriowo ya tuna aiki da Buhari
Da yake tuna lokacinsa a matsayin mai daukar hoton shugaban kasar, Omoboriowo ya bayyana cewa Buhari shugaba ne wanda ke da karfin gwiwa a kan tawagarsa kuma ya yarda da iyawarsu.
Ya bayyana cewa Buhari bai cika mayar da hankali sosai a kan hotunan ba amma yana da wani irin nasibi na daukar hotuna masu ban sha'awa.
Omobioriowo ya ce:
"Tsawon shekaru takwas, Shugaba Buhari bai taba neman na nuna masa hotunansa da na dauka ba.
"Idan ya zabe ka, ya yarda da iyawarka a kan wannan aiki...Kuma wannan shine wani abu na musamman game da shi; ya baka damar sannan zai bari ka yi yadda kake so."
Adesina ya bayyana halin tausayi da Buhari ya shiga
A wani labarin kuma, mun ji cewa Femi Adesina daya cikin masu magana da yawun Muhammadu Buhari, ya bada labari game da rashin lafiyar mai gidansa.
A littafin da ya rubuta a game da labarin gwamnatin Muhammadu Buhari, The Cable ta ce Femi Adesina ya tabo batun rashin lafiya.
Asali: Legit.ng