An Gano Ramin Karkashin Kasa Inda Masu Garkuwa Suke Ajiye Wadanda Suka Sace a Najeriya
- Gwamnatin jihar Anambra ta ce ta gano wani ramin karkashin kasa wanda masu garkuwa ke ajiye wadanda suka sace a ciki
- Gwamnatin ta ce ta gano ramin ne bayan da ta tura kayan aikin tonon kasa don gyara yankin Lokpanta da ke Umunneochi a jihar
- A baya-bayan nan ne 'yan bindigar da ke gudanar da ayyukan su a yankin suka mika wuya ga rundunar tsaro ta 'Operation Crush'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Anambra - Gwamnatin jihar Abia ta bankado wani boyayyen ramin da masu garkuwa da mutane ke ajiye mutane a Lokpanta da ke karamar hukumar Umunneochi a jihar.
Mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai Mista Ferdinand Ekeoma, ya ce jami’an tsaro na ‘Operation Crush’ ne suka gano ramin yayin da suka kai sumame yankin.
Ya bayyana cewa, an gano ramin da aka boye wadanda aka kama ne a yayin da gwamnati ta tura kayan aikin tonon kasa zuwa yankin, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“An gano wannan boyayyar ramin ne yayin da gwamnatin jihar karkashin Gwamna Alex Otti, ta tura kayan aikin tonon kasa domin share yankin.
"Hakan ya biyo bayan yadda mika wuya da ‘yan ta’adda suka yi ga undunar Operation Crush da ke samun goyon bayan gwamnati."
Da yake magana kan lamarin, shugaban karamar hukumar Umunneochi, Ndubuisi Ike, ya ce garkuwa da mutane ya ragu matuka a yankin, Daily Post ta ruwaito.
Matakin da Gwamna Otti ya dauka kan 'yan ta'adda
Mista Ike, wanda ya ce masu garkuwa da mutane sun lalata makarantu biyu kuma sun so mamaye yankin, ya kuma yaba wa Gwamna Otti da jami’an tsaro bisa kokarinsu.
A yayin kaddamar da rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta jihar Abia (Operation Crush), Gwamna Otti ya ba jami’an tsaro wani umarni.
Ya neme su da su tabbatar da cewa sun kama duk wasu masu aikata laifuka musamman masu garkuwa da mutane da ke yi wa al’ummar Umunneochi da sauran sassan jihar ta'addanci.
Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan Anambra
A wani labarin, hukumar EFCC ta saka ranar Laraba 24 ga watan Janairu, don gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Mr Willie Obiano.
Hukumar na zargin Mr Obiano da karkatar da naira biliyan hudu a lokacin da ya ke kan kujerar gwamnan Anambra.
Asali: Legit.ng