"Baturiya Na Ke Son Allah Ya Hallito Ni Idan Zan Sake Zuwa Duniya", In Ji Jarumar Fim Na Najeriya

"Baturiya Na Ke Son Allah Ya Hallito Ni Idan Zan Sake Zuwa Duniya", In Ji Jarumar Fim Na Najeriya

  • Fitacciyar jarumar Nollywood Destiny Etiko, jarumtacciyar matashiya ce wacce ke taka rawar gani a duk matsayin da aka daurata a fim
  • Jarumar ta tsoma baki cikin wani al'amari da ke magana kan dadin dake tattare da ace mace na cin gashin kanta
  • Etiko ta ce tana so Allah ya hallito ta a matsayin baturiya a rayuwarta ta gaba saboda duk da kasancewarta bakar fata bata jiran namiji ya dauki dawainiyarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jarumar fina-finan Kudu wato Nollywood, Destiny Etiko, ta bayyana cewa idan har Allah zai sake halitto ta a wata rayuwar, toh a baturi take so ta zo.

Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da take martani ga wani bidiyo da mai watsa shirye-shirye ta Instagram, Tunde Ednut ya wallafa, inda ya yan mata biyu dake bayani kan yancin cin gashin kansu, rahon Daily Trust.

Kara karanta wannan

Wani bature matukin jirgin sama ya garzaya Afrika don zabo mata daga kauye, ya aureta

Jarumar fim ta ce bariya take son zama a wata rayuwar
Ina son Allah ya hallito a matsayin baturiya/farar fata a wata rayuwar, Jarumar Najeriya Etiko
Asali: Instagram

A cikin bidiyon, yan matan sun bayyana cewa ba za su taba dogaro da maza don siya masu abubuwan bukata kamar su tsadaddun gashin yan kanti da gyaran jiki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma sun bayyana cewa sun fi son fitan sharholiya mai sauki da alkibla fiye da wanda za a je na wuce gona da iri.

A farar fata nake son fitowa a wata rayuwar, Etiko

Da take martani ga bidiyon, jarumar fim din ta bayyana cewa tana son fitowa a jinsin farar fata ne a rayuwarta ta gaba.

Ta kuma bayyana cewa duk da kasancewarta bakar fata yar Najeriya, bata jiran maza su yi mata abu amma tana karba idan suka zo.

Ta yi ikirarin cewa bata son samun amsa mara dadi a duk lokacin da ta nemi wani abu, don haka ta gwammaci ta yi kwadago ba ji ba gani don cimma mafarkanta, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

"A nemo mun ita: Bidiyon wata yar makaranta tana Sallah a kan hanya ya dauka hankalin jama'a

Etiko ta rubuta:

"A rayuwata ta gaba, a baturiya zan fito. Saboda duk da kasancewata yar Najeriya, bana tsammanin komai daga kowa, amma idan ya faru, babu laifi.
"Saboda na tsani jin A'A idan na bukaci wani abu, na gwammaci na yi aiki tukuru don cimma mafarkan rayuwata.
"Aikin neman kudina nake yi."

Jarumar fim ta caccaki mazan dake nemanta

A wani labarin kuma, mun ji cewa fitacciyar jarumar Nollywood, Uche Ogbodo ta yi martani ga mazan da ke damunta da sakonni a soshiyal midiya. Maza na damunta da zancen soyayya duk da cewar tana da igiyar aure a kanta.

Matar wacce ta haifi yara uku ta fada masu cewa tana da aure kuma jikinta na mijinta ne shi kadai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng