Filato: Yan Sanda Sun Harba Wa Korarrun Yan Majalisar PDP 16 Hayaki Mai Sa Hawaye
- Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa 'yan sanda sun watsa hayaki mai sa hawaye ga korarrun 'yan majalisar Filato su 16
- Hakan ya biyo bayan yunkurin da 'yan majalisun ke yi na ganin sun kutsa cikin ginin gidan gwamnati na Reyfiield, amma 'yan sanda sun hana
- Idan ba a manta ba, Kotun Daukaka Kara ta kori 'yan majalisar 16 da suka fito daga jam'iyyar PDP, lamarin da su kuma suka ki amince da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Filato - ‘Yan sanda dauke da makamai, a ranar Talata, sun harba barkonon tsohuwa ga ‘yan majalisar dokokin jihar Filato su 16 da kotun daukaka kara ta kora.
‘Yan majalisar sun isa tsohon ginin gidan gwamnatin jihar na Rayfield da ke Jos a safiyar ranar Talata tare da magoya bayansu da nufin komawa zauren majalisar a lokacin da lamarin ya faru.
'Yan sanda da sauran jami'an tsaro sun mamaye harabar gidan gwamnati tare da hana 'yan majalisar da aka kora shiga zauren majalisar, rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai Pulse Nigeria ta gano cewa ‘yan majalisar sun sha alwashin ba za su fice daga harabar ba, har sai sun shiga matsayin halastattun 'yan majalisu.
Gwamnan Filato ya saka dokar ta-baci a Mangu
A hannu daya kuma, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya saka dokar ta-baci na awanni 24 a karamar hukumar Mangu da ke jihar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan watsa labarai na gwamnan, Gyang Bere, da aka fitar a ranar Talata.
Ya ce saka dokar ta ɓacin ya biyo bayan tabarbarewar tsaro da aka samu a karamar hukumar.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnan ya nemi al'ummar karamar hukumar Mangu da su bi wannan umarni sau da kafa don ba jami'an tsaro damar wanzar da zaman lafiya a yankin.
"Gwamnan ya lura cewa akwai wasu bata gari da ke son haddasa rikici a jihar, duk da kokarin sa na ganin an dakile duk wani aikin ta'addanci."
Mutfwang ya kuma jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa tare da basu tabbacin kokarin gwamnati na wanzar da zaman lafiya a jihar.
Asali: Legit.ng