Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sanye da Kakin Sojoji, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Jihar Arewa
- Yan bindiga sanye da kakin soji sun yi awon gaba da bayin Allah sama da 30 a yankin ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina
- Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun yaudari jama'a da sunan jami'an tsaro ne aka turo su ba su kariya
- A cewar wani mutumi, sai da ƴan ta'adda suka gama tara jama'a sannan suka tasa ƙeyarsu zuwa cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Miyagun 'yan bindiga sanye da kakin sojoji sun yi garkuwa da wasu mutanen kauye 31 a wani hari da suka kai kauyen Tashar Nagule, ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Wata majiya mai tushe a yankin ta bayyana cewa ‘yan bindiga da yawa sun kutsa kai cikin ƙauyen ba zato ba tsammani sanye da kayan sojoji a daren Lahadi.
Ya ce bayan gama tsara kansu, maharan sun tattara mazauna ƙauyen da suka ƙunshi mata da kananan yara, suka yi awon gaba da su, jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan bindigan suna yaudari mutanen ƙauyen
Mutumin ya yi bayanin cewa da farko ƴan ta'addan sun kewaye kauyen kana daga bisani suka aiko wasu daga ciki suka shigo suka tafi da mutane kusan 31.
Ya ce:
"Muna zaune a ƙofar gida ni da abokaina wajen karfe 9:00 na daren kwatsam muka fara jin ƙarar harbe-harben bindiga. Mun tashi zamu gudu amma maharan suka daka mana tsawa.
"Suka gaya mana jami'an tsaro ne aka turo su tsare mu, sun san idan suka ce ƴan sanda ne ko sojoji aka turo mana zamu yarda da su, kuma abinda ya faru kenan."
Majiyar ta ƙara da cewa bisa haka yan ƙauyen suka fara taruwa a dandali ba tare da sanin waɗannan mutanen da ke sanye da rigar sojoji ba jami'an tsaro bane ƴan bindiga ne.
"Lokacin da ‘yan ta’addan suka zagaye mutanen garin, sai suka ce su bi su cikin dajin, a lokacin muka gane ba jami’an tsaro ba ne. Na faki ido na fice da gudu zuwa gida."
Ya ce zuwa yau Litinin, sun tantance mutane 31 da maharan suka yi awon gaba da su. Ƴan bindigan sun haɗa da wasu da suka gudu zuwa jeji don neman tsira.
Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba dangane da sabon harin da aka kai, rahoton The News.
Yan bindiga sun kashe magajin gari a Neja
A wani rahoton na daban Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari, sun kashe magajin gari tare da sace wasu sama da 10 a jihar Neja.
Shugaban ƙaramar hukumar Munya, Aminu Najume, ya ce ƴan ta'addan sun fito ne daga ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
Asali: Legit.ng