Bincike Ya Gano Jihohin Najeriya 10 da Aka Fi Samun Man Fetur da Araha
- Sabbin bayanai daga NBS sun bayyana kididdigar yadda ‘yan Najeriya ke fama da tsadar man fetur da yadda suke saye
- Bayanan sun kuma bayyana cewa, ana siyar da man fetur a Najeriya a kan farashin da akalla bai yi kasa da N600 ba
- A cewar kididdigar ta NBS, jihar Kano ce aka fi samun mai da araha, daga nan kuma sai jihar Legas da ke mataki na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Kididdigar hukumar NBS ta bayyana alkaluman farashin man fetur a Najeriya da yadda aka siyar dashi zuwa karshen watan Disamban bara; 2023.
A cewar kididdigar, an siyar da man fetur a kan farashin N671.86 a watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2023.
Wannan na nuni da karin 225.86% idan aka kwantanta da N206.19 da aka siyar da man a watan Disamban shekarar 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe wannan rahoton ya firo?
Wannan na zuwa ne a sabon rahoton da ke bayyana farashin kayayyaki da NBS ta wallafa, wacce Legit ta samo a karshen makon nan.
Rahoton ya kuma nuna cewa adadin kudin da masu motoci a Najeriya suka kasha a mai a watan Disambar 2023, inda rahoton yace adadin ya karu da 3.53% daga N648.93 da suka siya a watan Nuwamban 2023.
Farashin man fetur ya bambanta da jihohi
Bugu da kari, NBS ta yi wani bincike na jihohi inda ta nuna cewa jihar Kano da jihar Legas da Adamawa ne suka fi arahar man fetur a Najeriya.
A gefe guda kuma, mazauna Ogun, Taraba da Adamawa sun siya mai a farashi mafi tsada a watan Disamban 2023, in ji rahoton.
Farashin mai a Disamban 2023 a jihohin Najeriya 10
- Kano N602.78
- Legas N612.72
- Borno N622.71
- Oyo N626.56
- Delta N640.00
- Osun N641.54
- Ondo N644.06
- Kwara N650.63
- Ekiti N653.44
- Benue N658.89
Farashin mai a yankunan Najeriya
- Arewa ta tsakiya N657.69
- Kudu maso Yamma N659.14
- Kudu maso kudu N666.05
- Arewa maso yamma N672.30
- Kudu maso Gabas N679.75
- Arewa maso gabas N699.82
An fara neman sanya hannun jari a matatar Dangote
A wani labarin, bayan sanar da cewa matatar man Dangote ta fara aiki, masu saka hannun jari sun garzaya zuwa kasuwar canji ta Najeriya don siyan hannayen jari na rukunin Dangote.
Bayan haka, darajar wasu rassa uku na rukunin Dangote da aka saka a kan kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya (NGX) ta karu da naira biliyan 513.69 a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng