Wata Sabuwa: Gwamnan Jiha Ya Hana Amfani da Robobin Abinci a Jiharsa, Ya Fadi Dalili

Wata Sabuwa: Gwamnan Jiha Ya Hana Amfani da Robobin Abinci a Jiharsa, Ya Fadi Dalili

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya sanar da haramta amfani da robobin abinci na “takeaway” a ilahirin jihar
  • Ya bayyana hakan ne ta bakin kwamishinan muhalli na jihar, Tokumbo Wahab, inda yace hanin ya fara aiki nan take
  • Gwamnati ta kafa hujjar cewa, irin wadannan robobi ba sa narkewa a kasa, don haka barazana ce yga muhalli a nan gaba kadan

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Ikeja, jihar Legas Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya haramta amfani da robobin abinci ‘kudinka a bola’ da aka fi sani da ‘takeaway’ duba da yanayi na tsaftar muhalli.

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi 21 ga watan Janairun 2023 ta bakin kwamishinan muhalli Toknbo Wahab.

Kara karanta wannan

An shiga mummunan yanayi a Legas, gobara ta yi kaca-kaca da wani bene mai hawa 10

Sanwo Olu ya hana amfani da robobin abinci a Legas
An haramta amfani da robobin abinci a Legas | Hotuna: Pexel, Babajide Sanwo-Olu (X)
Asali: UGC

A sanarwar da kwamishinan ya yada a shafinsa na X, ya bayyana dalili da kuma abin da gwamnati ta hango kafin haramta amfani da robobin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hangen gwamnatin Legas

A sanarwar, y ace:

“Biyo bayan barazanar da robobin da ake amfani dasu sau daya ke jawowa, musamman Styrofoam da bas a narkewa, suna haddasawa matsala ga muhalli, gwamnatin jihar Legas (@followlasg) ta hannun ma’aikatar muhalli da albarkatun ruwa (@LasgMOE) ta sanar da dakatar amfani dasu a fadin jihar.”

Jihar Legas dai na daga jihohin Najeriya mafi cunkoso da ake yawan amfani da irin wadannan robobin abinci ba kakkautawa.

Sai dai, ba wannan ne karon farko da ake hakan ba a Najeriya, an samu gwamnan da ya haramta amfani da leda da robobi a jiharsa.

Gwamna ya hana amfani da bakar leda a jiharsa

A wani labarin luma, kunji yadda gwamnan jihar Taraba ya haramta amfani da bakar leda a jiharsa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani 'Bam' ya tashi da mutane a jihar arewa, ya tafka mummunar ɓarna

A yayin da kabilun Taraba da Benue ke cigaba da baiwa hammata iska wanda hakan yayi sanadiyyar asarar rayuka da dimbin dukiya a tsakaninsu, shi kuwa gwamnan Taraba, Darius Ishaku ba wannan matsalar ce a gabansa ba.

Legit.ng a 2019 ta ruwaito gwamnan Taraba, Darius Ishaku ya haramta amfani da bakar leda a kwata, kai bama bakar leda ba, kowanne irin ledar amfani yau da kullum da duk wata jakar da aka sarrafata da roba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.