Kowa da matsalarsa: Wani gwamnan Arewa ya haramta amfani da bakar leda a jaharsa

Kowa da matsalarsa: Wani gwamnan Arewa ya haramta amfani da bakar leda a jaharsa

A yayin da kabilun jahar Taraba da na jahar Benuwe ke cigaba da baiwa hammata iska wanda hakan yayi sanadiyyar asarar rayuka da dimbin dukiya a tsakaninsu, shi kuwa gwamnan jahar Taraba, Darius Ishaku ba wannan matsalar bace a gabansa.

Legit.ng ta ruwaito gwamnan jahar Taraba, Darius Ishaku ya haramta amfani da bakar leda a jahar Taraba kwata, kai bama bakar leda ba, kowanne irin ledar amfani yau da kullum da duk wata jakar da aka sarrafata da roba.

KU KARANTA: Yan Shia sun harba nukiliya kasar Makkah yayin da Musulmai ke gudanar da Umarah

Kowa da matsalarsa: Wani gwamnan Arewa ya haramta amfani da bakar leda a jaharsa

Darius
Source: Twitter

Darius Ishaku ya bayyana cewa yayi wannan doka ne domin shawo kan barazanar da ledoji ke yi ma muhalli a jahar Taraba, kamar yadda ya bayyana a yayin kaddamar da tsarin tsaftace ruwa, tsaftace muhalli da kuma tsaftar jiki.

Gwamnan ya bada tabbacin nan bada jimawa ba zai aika da kudurin dokar haramta amfani da leda a jahar Taraba ga majalisar dokokin jahar domin ta samu amincewarsu ta yadda zama tabbatacciyar doka mai zaman kanta.

Haka zalika gwamnan ya bayyana godiyarsa bisa kokarin samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jahar da hukumar bada tallafi ta kasar Amurka, USAID da na kasar Japan JAICA suke yi, don haka ya bukaci hukumar ruwan sha ta jahar data tabbata ta kula da lafiyar bututun dake kai ruwa ga jama’a a jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel