NAFDAC ta dakatar da kamfanin ruwan roba na ‘Eva Premium Table water’

NAFDAC ta dakatar da kamfanin ruwan roba na ‘Eva Premium Table water’

-NAFDAC ta dakatar da kamfanin sarrafa ruwan roba na Eva premium table water a bisa dalilin rashin ingancinsa

-Duk a cikin wannan labarin zaku ji cewa hukumar ta garkame wani kamfani a Abuja inda ake sarrafa zuma ta jabu ba tare da yin rajistar kamfanin ba

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa wato NAFDAC ta dakatar da ayyukan kamfanin ruwan roba mai suna ‘Eva premium table water’ dake kauyen Asejire a jihar Oyo a bisa rashin ingancin ruwan.

NAFDAC ta sanar da wannan matakin ne ta hanyar amfani da shafinta na Tuwita. Mutane da dama sun yi ta kai kukan su ga hukumar game da rashin ingancin ruwan inda suka ce ana ganin datti cikin ruwan a wani lokaci ma har sauya kala ruwan ke yi.

KU KARANTA:An kama wata mata na zina da wanda ya kashe mijinta

Hukamar NAFDAC ta ce: “ Tabbas wannan kamfanin ya yi rajista da mu, kuma sun san da dukkanin sharuddanmu saboda mun ba su takarda mai kunshe da sharuddan.

“ Wadannan sharuddan sun hada da sarrafa ruwan da bashi da kala, baya wari sannan kuma babu datti a cikinsa.”

NAFDAC ta bada bayanin cewa wannan kamfanin zai cigaba da ayyukansa ne bayan hukumarsu ta kammala bincike a kansa.

Haka zalika, hukumar ta yi kira ga ‘yan kasuwan dake dillancin wannan ruwa da su daina sannan kuma wanda ke a hannunsu su maida zuwa kamfanin.

Har ila yau, a cikin kwanakin baya ne NAFDAC ta kama wani kamfanin dake sarrafa jabun zuma mai suna ‘Up the Rock Church of God’ a Durumi Abuja.

Shugaban hukumar NAFDAC, Moji Adeyeye ce ta bada sanarwar dakatar da wannan kamfanin, inda take cewa an dakatar da kamfanin ne bisa laifin rashin yin rajista da hukumarsu da kuma yin amfani da wuri maras tsafta domin sarrafa zumar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng