Yan Bindiga Sun Sako Karin Mutanen Abuja da Suka Yi Garkuwa da Su

Yan Bindiga Sun Sako Karin Mutanen Abuja da Suka Yi Garkuwa da Su

  • Ƴan bindiga sun saƙo karin mazauna birnin tarayya Abuja da suka yi garkuwa da su tun ranar Lahadin da ta wuce
  • Tun farko mahara sun yi awon gaba da mutum 10 yayin da suka kai hari Sagwari Estate a karamar hukumar Bwari, sun kashe 3 daga ciki
  • Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa sauran mutane bakwai sun shaƙi iskar yanci daga hannun masu garkuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mutane bakwai da aka sace a rukunin gidajen Sagwari da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shaƙi iskar ƴanci daga hannun masu garkuwa.

Daily Trust ta tattaro yadda ‘yan bindiga suka kai samame Unguwar da ke gaban makarantar sakandaren mata ta gwamnati (GGSS) Dutse, da misalin karfe 8 na daren Lahadi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani 'Bam' ya tashi da mutane a jihar arewa, ya tafka mummunar ɓarna

Yan bindiga sun sako mutanen Abuja.
Yan Bindiga Sun Sako Karin Mutanen Abuja da Suka Yi Garkuwa da Su Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Yayin wannan harin, ƴan bindigan suka yi awon gaba da wasu mutane 10 zuwa maɓoyarsu da babu wanda ya sani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan sun kashe wasu daga ciki da suka haɗa da ɗalibar 500 Level a jami'ar Bayero (BUK), Talatu Salihu, ma'akaciyar Otal, Akpagher Joseph Terzungwe da yar shekara 13, Mitchell Ariyo.

Bayan kashe su, masu garkuwan suka ƙara yawan kuɗin fansar sauran da ke hannunsu, sannan suka sanya wa'adin ranar Laraba, The Cable ta ruwaito.

Sauran mutane 7 sun koma gida

Wasu majiyoyi daga Anguwar sun bayyana cewa ragowar mutanen da maharan suka sace sun kubuta, kuma har sun koma cikin danginsu.

Waɗanda yan bindigan suka sako sun kunshi, mai ƙarbar baƙi a otal mace, uwa da yaranta uku, da kuma wasu ƙananan yara uku.

Majiyar ta ƙara da bayanin cewa masu garkuwan sun tura wa iyalan mutanen wuraren da suka je suka ɗauko ƴan uwansu daban-daban.

Kara karanta wannan

"Taku ta ƙare" An kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi mutanen Abuja

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan sauran ‘yan uwan marigayiya Nabeeha Al-Kadriyah 4, wacce ƴan bindiga suka kashe, sun kuɓuta.

Maharan sun sace ƴan uwan juna mata tare da mahaifinsu a watan Janairu, inda suka sa wa'adin biyan fansa, bayan ya wuce suka kashe Nabeeha.

Buhari ya yi magana kan shugaban IPOB

A wani rahoton kuma tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce gata gwamnatinsa ta yi wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB.

A littafin da tsohon kakakin Buhari, Femi Adesina ya rubuta, Buhari ya faɗi yadda gwamnatinsa ta taso ƙeyar Kanu zuwa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262