Fashola Ya Bayyana Yawan Kudin da Yake Karba a Matsayin Fansho Daga Gwamnatin Legas, Bidiyon Ya Yadu

Fashola Ya Bayyana Yawan Kudin da Yake Karba a Matsayin Fansho Daga Gwamnatin Legas, Bidiyon Ya Yadu

  • Babatunde Fashola ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan bayyana abun da yake karba duk wata a matsayinsa na tsohon gwamna
  • Tsohon gwamnan Legas din ya bayyana a wata hira da aka yi da shi cewa N577,000 kacal yake karba duk wata daga gwamnatin jihar
  • Fashola ya bayyana hakan ne sabanin abun da ake rade-radi inda ya kuma karyata karbar biliyoyi daga gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon ministan ayyuka da gidaje kuma tsohon gwamnan Legas, Babatunde Raji Fashola, ya yi karin haske dangane da kudin fanshon da gwamnatin jihar ke biyansa duk wata.

Fashola ya karyata karbar biliyoyi daga gwamnatin tarayya
Fashola Ya Bayyana Yawan Kudin da Yake Karba a Matsayin Fansho Daga Gwamnatin Legas, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Babatunde Raji Fashola
Asali: Facebook

Fashola, wanda ya bayyana a matsayin bako a shirin Arise TV, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin jihar Legas na biyansa N577,000 a matsayin fansho duk wata.

Kara karanta wannan

"Ba su gane shi ba": Hamshakin mai kudi Femi Otedola ya shiga motar haya a wani tsohon bidiyo

Tsohon ministan ya bayyana cewa duk da labaran da ke yawo cewa yana karbar biliyoyi a matsayin fansho daga gwamnatin jihar, abun da yake karba duk wata N577,000 ne kacal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fashola ya ce:

“Amfanin da nake samu shi ne ina ganin kudin fansho N577,000 daga jihar Legas duk wata, abin da nake samu ke nan kuma duk da labaran cewa muna samun biliyoyi da dama, na fito na musanta hakan sau da dama.
"To ban san tsawon lokacin da zai dauka ba amma duk wata ina samunsa. Abin da nake samu ke nan kuma babu wata moriya daga gwamnatin tarayya kwata-kwata.”'

Kalli bidiyon a kasa:

Yan Najeriya sun martani ga bayanin Fashola

Kamar kullun yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi don yin martani kan ci gaban. Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

@ChrisEjiofor7 ya rubuta:

"Duk lokacin da suka fadi gaskiya, za ka gane."

@EAsije ya rubuta:

"Nawa ma'aikatan gwamnati da suka yi riya a jihar Legas suke karba a matsayin fansho?"

@I_like_Ebuka ya rubuta:

"Basa taba fadin gaskiya."

Shehu Sani ya yi martani kan littafin Buhari

A wani labari na daban, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya ce yan Najeriya basa bukatar karanta littafin nan da tsohon mai magana da yawun shugaban Muhammad Buhari wato Femi Adesina ya wallafa.

Shehu Sani wanda dan gwagwarmaya ne, ya ce tuntuni mulkin shekaru takwas din Buhari ya zama jiki magayi, domin kuwa ko dan yaro ya san cewa an yi mulki a wannan lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng