Yadda Kwakwalwar Matashi Ta Koma Fanko Bayan Kwanciya da 	Budurwa, Labarin Ya Girgiza Jama’a

Yadda Kwakwalwar Matashi Ta Koma Fanko Bayan Kwanciya da Budurwa, Labarin Ya Girgiza Jama’a

  • Wani dan Najeriya ya bayyana mawuyacin halin da ya shiga bayan ya yi mu'amalar kwanciya da wata matashiyar budurwa
  • Bayan sun gama tarayyar kwanciya, sai matashin wanda dalibi ne ya shiga dakin zana zarrabawa amma sam ya gaza rubuta komai a takardarsa na amsa tambayoyi
  • Jama'a da dama sun tausaya ma dalibin a dandalin X yayin da labarin nasa ya bai wa wasu dariya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani dan Najeriya ya ba da labarin yadda sharholiyarsa ya kai shi ya baro tare da jefa shi cikin wani mawuyacin hali.

Matashin mai suna Aloysius Bello ya tuna yadda kwakwalwarsa ta koma tamkar fanko a cikin dakin zana jarrabawa.

Daga sharholiya kwakwalwar matashi ta koma tamkar fanko
An yi amfani da Hotunan don misali ne kawai Hoto: Liba Taylor, KOLA SULAIMON/ Getty Images.
Asali: Getty Images

Matashi ya shiga yanayi bayan kwanciya da budurwa

Kara karanta wannan

"Ba su gane shi ba": Hamshakin mai kudi Femi Otedola ya shiga motar haya a wani tsohon bidiyo

A cewar Aloysius, duk da cewar ya shirya ma jarrabawar, ya shiga dakin zana jarrabawar sannan kwatsam kwakwalwarsa ta koma fanko babu komai ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tsinci kansa a cikin wani yanayi mai cike da takaici saboda tasirin kwanciyar da ya yi kan kwakwalwarsa.

Ya tuna yadda ya gaza rubuta koda kalma guda ce a kan takardar amsarsa a dakin jarrabawar bayan ya kwanta da matashiyar.

Da yake ba da labarin a dandalin X, ya bayyana haduwarsa da budurwar a matsayin kwanciya mafi muni a rayuwarsa.

Jama'a sun yi martani

Chukason ya ce:

"Baaba wannan ba karamin abu bane. Abun ya yi maka dadi da yawa ne ko dai menene."

SarahMatthew ta yi martani:

"Wannan ya yi kama da akwai surkulle ciki. Me zai sa ba za ka yi rubutu ba."

Jenifaaa ta yi martani:

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

"Allah dai ya kyauta. Maza kuna ganin abu dai."

OluwafemiOla ya yi martani:

"Wannan ya tuna mani da abun da ya same ni amma ba zan fade shi a kan Twitter ba."

Matashiya ta ci karo da shinkafa a mitifie

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya bayan ta gano shinkafar dafa-duka a cikin cincin din 'mitifie' da ta siya N50.

Ta garzaya dandalin TikTok don baje kolin cincin din da abun da ya kunsa a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng