Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Sojoji da Mutanen Gari
- Tsaregun yan bindiga sun kai mummunan hari tare da kashe mutanen gari ciki harda sojoji a yankin Agatu da ke jihar Benue
- Jami'an sojoji biyu da wasu mazauna kauyen biyu sun mutu lokacin da sojoji da yan bindihar suka yi musayar wuta a yankin, mazauna garin suka bayyana
- Lamarin tsaro a karamar hukumar Agatu da ke jihar Benue ya tabarbare sakamakon wannan sabon farmakin da yan bindiga suka kai
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wasu yan bindiga da ake zaton makiyaya ne sun kai mummunan hari a Makurdi, babban birnin jihar Benue.
Yadda yan bindiga suka kashe mutum hudu
A kalla mutane hudu, ciki harda sojoji biyu aka kashe a wani hari da yan bindiga suka kai garin Okokolo a karamar hukumar Agatu ta jihar Benue.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen gari sun sanar da jaridar Daily Trust cewa jami’an sojojin na kokarin dakile hare-hare da dama da aka kai wa garuruwan Agatu a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, ne lokacin da yan bindigar suka kai masu harin kautan bauna.
Sannan suka kashe sojoji biyu, inda suka bar wani daya da mummunan rauni inda aka kwashe shi zuwa asibiti a Makurdi.
Da yake magana a madadin mutanen Agatu a majalisar dokokin jihar, Godwin Abuh Edoh, ya tabbatar da cewar an kashe mutum biyu a harin sannan wasu da dama sun jikkata, rahoton Vanguard.
Sai dai kuma, ya ki yin martani game da sojin, inda ya nanata cewa: "ba ma rubutawa rundunar sojoji mutuwar sojoji."
A halin da ake ciki, rundunar sojin karkashin jagorancin jami’in hulda da jama’a na Brigade 401, Kyaftin Grutus da takwaransa na Operation Whirl Stroke (OPWS), Flight Laftana Oquoh, ba su yi martani kan lamarin ba.
Yan bindiga sun farmaki rukunin gidajen Sojoji a Abuja
A wani labarin kuma, mun ji cewa masu yan bindiga sun kai hari a rukunin gidajen sojojin Najeriya da ke Abuja a daren ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da mutane biyu.
Lamarin ya faru da misalin karfe 10 na dare a unguwar Phase 2 , inda masu garkuwan suka sace wata mata da daya daga cikin surukan wani Barista Cyril Adikwu.
Asali: Legit.ng