“Abun Kunya Ne”: Shugaban EFCC Ya Fallasa Masu Bincike da ke Karbar Na Goro, Ya Bada Sabon Umurni
- Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya yi sabon barazana ga masu gudanar da bincike na hukumar
- Hakan na zuwa ne yayin da ya nuna fushinsa kan irin cin hanci da rashawa da masu bincike na hukumar ke tafkawa
- Sai dai kuma, Olukoyede ya fitar da sabbin umarni game da "kamu da bayar da beli" yakuma sha alwashin yin maganin duk wanda ya ki bin dokar hukumar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya zargi wasu jami’an hukumar wadanda ke kula da bangaren binciken masu laifi, da karbar na goro.
Shugaban EFCC din ya zarge su da aikata hakan ne a yayin gudanar da ayyukan da doka ta rataya musu.
Olukoyede ya ce dole ne yanzu aikin dake gabansa ya takaita ga kokarin kawar da su daga cikin hukumar, ko kuma dai su sauya zuwa mutane na gari, sabanin yadda suke a yanzu, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, yayin da yake gabatar da sakon sa na sabuwar shekara ga jami’an hukumar, a shelkwatar hukumar dake Abuja, rahoton Punch.
Abun kunya ne, EFCC ta koka kan wasu jami'anta
Ya kara da cewa bayyanar wannan lamari a tsakanin jami’an hukumar babban abun kunya ne, duba ga cewar duniya tana kallon hukumar a matsayin wata kafa mai kokarin dakile wannan barna.
Olukoyede ya kuma ce tuni ya umarci sashin kula da harkokin cikin gida na hukumar, akan ya ci gaba da sanya ido domin bankado ire iren wadancan bata gari, tare da tabbatar da daukar mataki mai tsauri ga duk wanda aka samu da aikata badakala.
Daga nan sai ya gargadi dukkan masu irin wannan dabi’a akan su zama mutane na gari abun koyi, wanda hakan zai sanya su karawa hukumar daraja a idon duniya.
Shugaban na EFCC ya ce:
“A wannan gabar nake aikewa da sakon gargadi mai karfi ga duk wanda yake aiki karkashin mu kuma yake saba ka’ida, akan cewa lokaci yayi da zasu zama mutanan gari ko kuma mu mayar da su mutane na gari.”
Kotu ta garkame tsohon dan majalisar Kaduna
A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa an garkame Suleiman Dabo, tsohon dan majalisar dokokin jihar Kaduna (Mazabar Zaria) a gidan yari na Kuje har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan neman belinsa.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ne ya ba da umarnin a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng