Basaraken Abuja da Aka Yi Garkuwa da Shi a 2023 Ya Kubuta, an Biya Naira Miliyan 8 Kudin Fansa
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun sako basaraken Abuja da mukarrabansa guda 5 bayan biyan kudin fansa
- An ruwaito cewa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, sun biya Naira miliyan takwas tare da tabar wiwi da katin waya na naira 437,000
- Tun a watan Disambar shekarar 2023 ne 'yan bindigar suka kutsa fadar basaraken suka yi awon gaba da shi da mutane biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT Abuja - Dagacin garin Pandan-Gwari da karamar hukumar Bwari, FCT Abuja, Ezekiel Baba da wasu mutum biyar sun samu 'yanci bayan biyan naira miliyan takwas ga wadanda suka kama su.
City & Crimes ta ruwaito cewa a ranar 26 ga watan Disamba, 2023 ne 'yan bindiga suka shiga har fada suka sace basaraken da mukarrabansa guda biyar.
Yan bindigar sun nemi wiwi, barasa da katin waya
Da ya ke tabbatar da sakin basaraken da mukarrabansa a ranar Laraba, wani mazaunin garin Kawu, Usman Yakubu ya ce 'yan bindiga sun saki basaraken a dajin Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Yakubu na cewa:
"Baya ga naira miliyan takwas da aka biya, sai da aka hada masu da tabar wiwi, barasa da katin waya na naira dubu 437."
Yakubu ya kara da cewa yanzu haka basaraken na kwance a asibiti yana jinyar rashin lafiya.
A ranar Talata, 9 ga watan Janairu ne wani daga cikin iyalan basaraken, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa 'yan bindigar sun nemi naira miliyan 50 matsayin kudin fansar mutanen shida.
Sai dai bayan dogon lokaci ana ciniki da 'yan bindigar, sun amince a biya naira miliyan 8 don sako basaraken da mukarrabansa biyar.
Yan sanda sun kubutar da mutumin da aka sace a Abuja
A wani labari makamancin wannan, rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kubutar da wani mutum mai suna Segun Akinyemi daga hannun masu garkuwa da mutane a ranar Alhamis.
Kakakin rundunar na jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ya sanar da hakan, yana mai cewa 'yan sandan sun samu rahoton cewa masu garkuwar za su wuce da mutumin ta hanyar Kaduna.
Bayan samun wannan rahoto, jami'an rundunar sun tare 'yan bindigar inda suka yi musayar wuta, a karshe suka kubutar da Akinyemi tare da kama wasu daga cikin masu garkuwar.
Asali: Legit.ng