Yan Sanda Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace a Abuja, an Kama Mai Garkuwan
- Rundunar'yan sanda ta ce jami'anta sun yi musayar wuta da gungun wasu 'yan bindiga a hanyar Kaduna a ranar Alhamis
- A cewar kakakin rundunar na jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, rundunar ta samu rahoton 'yan bindigar za su wuce da wani mutum zuwa Kano
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi garkuwa da wani Segun Akinyemi a Abuja, kuma 'yan sandan sun kama wasu daga cikin su
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kaduna - An yi musayar wuta mai zafi, a ranar Alhamis, yayin da ‘yan sanda suka kubutar da Segun Akinyemi, wani mazaunin Abuja, tare da kama wasu daga cikin 'yan bindigar.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindinga sun yi garkuwa da Akinyemi ne a dai dai lokacin da yake fita daga gidansa a mota.
Masu garkuwa da mutanen suna kokarin daukar Akinyemi daga Abuja zuwa jihar Kano a lokacin da ‘yan sanda suka yi masu kawanya, inda suka yi musayar wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun fafata da masu garkuwa
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce a ranar 18 ga watan Janairu, 2024, jami’an da ke aiki a hedikwatar Kawo, Kaduna, sun samu kiran gaggawa na wani yunkurin garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Ya ce an sanar da su cewa 'yan ta'addan da wanda aka kama na kokarin wucewa ta hanyar Kaduna, lamarin da ya saka suka kai agajin gaggawa don dakile tafiya da mutumin.
Yan bindiga sun sace wata mata da ɗanta a Zariya
A wani labarin kuma, 'yan bindiga sun shiga garin Doguwa da ke cikin karamar hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna, kuma sun yi awon gaba da wata mata da ɗanta.
An ruwaito cewa 'yan bindigar ba su yi sa ar kama mijin ba mai suna Mallam Bello, wanda aka ce ya tsere bayan da ya ji 'yan bindigar sun kawo farmakin.
Har zuwa yanzu dai babu wani bayani daga 'yan bindigar kan neman kudin fansa, amma rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin.
Asali: Legit.ng