Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Afkawa Kauyuka 10 a Karamar Hukuma a Kaduna
- Ƴan bindiga sun afkawa mutanen ƙauyuka 10 da ke ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a yankin Arewa maso Yamma
- Ƴan bindigan dai sun kori mutanen ƙauyukan na yankin Kidandan daga gidajensu da ƙarfi da yaji
- Mutanen ƙauyukan dai sun bar gidajensu da abincinsu inda suka koma rayuwa a wasu ƙauyukan da ke da dama-dama wajen tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun kori mutanen ƙauyuka 10 daga muhallansu a yankin Kidandan da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Giwa dai na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Jaridar Daily Trust ta ce wasu daga cikin mazauna ƙauyukan, an tilasta musu yin ƙaura zuwa garin Kidandan da sauran ƙauyukan da suka fi tsaro a ƙaramar hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Tunburktu Hayin Dabino, Mugaba, Nasarawan Hayin Doka, Dokan Yuna, Doka, da Hayin Teacher.
Kansilan Kidandan, Abdullahi Ismail, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya koka da cewa a cikin makonni uku da suka gabata sojoji suna gudanar da ayyuka a kewayen yankin amma har yanzu ƴan bindigan na ci gaba da addabar wasu ƙauyukan.
Mutanen yankin sun koka kan halin da suke ciki
Wani shugaban al’umma, wanda ya gwammace a sakaya sunansa, ya ce mazauna ƙauyukan da suka rasa matsugunnansu sun bar kayan abinci da gidajensu saboda tsangwama da ƴan bindiga ke musu a kai a kai.
Ya kuma bayyana cewa sojoji da ke aiki a yankin sun kashe mutum shida daga cikin ƴan bindigan ranar Talata.
Ya bayyana cewa duk da cewa mazauna yankin sun yi farin ciki da kashe ƴan bindigar, amma sun yi shakkar nuna murnarsu a fili.
Ya buƙaci gwamnati ta ƙara tura jami’an tsaro domin hana ƴan bindigan korar mutanen sauran ƙauyukan.
Ba a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba, ASP Mansir Hassan, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Mutane Sun Tsere Daga Gidajensu a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutanen wasu ƙauyuƙa 10 na jihar Zamfara sun gudu sun bar gidajensu.
Mazauna ƙauyukan da ke a ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar sun gudu ne kan fargabar fuskantar hare-hare daga ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga.
Asali: Legit.ng