Iyalan Nabeeha Sun Bayyana Halin da Suke Ciki Bayan Cikar Wa’adin Karbo Yan Uwanta
- Wa'adin da yan bindiga suka dibar wa iyalan Al-Kadriyar don karbo sauran yan matansu da ke tsare a hannunsu ya cika
- Iyalin sun ce suna zaman jiran amsa kiran yan bindigar yayin da hankalinsu yake a tashe don rashin sanin da wacce za su zo
- Tun farko dai maharan sun kashe daya daga cikin yan matan, Nabeeha saboda rashin biyan kudin fansar da suka bukata na miliyoyin naira
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Iyalan Nabeeha Al-Kadriyar, yarinyar da yan bindga suka kashe a Abuja, sun ce suna cikin tashin hankali yayin da wa’adin da aka diba masu na biyan kudin fansar yan uwanta ya cika.
A makon jiya ne yan bindigar suka kashe Nabeeha daya daga cikin yan matan da ke tsare a hannunsu su shida, sakamakon rashin biyan kudin da suka nema daga yan'uwan yaran.
Bayan sun kashe ta sai maharan suka kuma kara kudin fansar yan uwanta daga naira miliyan 60 zuwa miliyan 100 sannan suka nemi a biya zuwa ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muna jira cike da tashin hankali, iyalin Nabeeha
Asiya Adamu, wadda ta zanta da sashin Hausa na BBC a madadin iyalin yaran, ya bayyana cewa suna zaman jiran samun kira daga wajen yan bindigan don jin mataki na gaba.
A cewar Asiya, sun iya bakin yin su, sai dai kuma yanzu suna zaman jiran jin wani umurni yan ta’addan za su bayar.
BBC ta nakalto Asiya na cewa:
"Hankalin kowa a tashe yake, muna zaman jira, mun yi kewar su. Kawai dai muna son mu ga sun dawo."
Haka kuma, ta ce a duk sanda maharan suka kira, su kan sada yan matan da iyayensu ta waya domin su yi magana tare da sanar da su halin da suke ciki, da neman a yi gaggawan biyan kudin fnsarsu.
Yaushe aka sace yan matan?
A ranar, 2 ga watan Janairu, ne yan bindigar suka yi garkuwa da yan matan su shida da mahaifinsu a yankin Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja.
Daga bisani sai maharan suka sako mahaifinsu domin ya je ya tattara kudin fansarsu na miliyoyin kudi, sai dai suka kashe Nabeeha kafin a kai ga hada kudin.
FG ta yi gargadi kan biyan kudin fansa
A baya mun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta gargadi matakin tara kudi don biyan kudaden fansa ga 'yan bindiga a kasar.
Ministan tsaro, Badaru Abubakar shi ya bayyana haka inda ya ce matakin zai kara rikirkita matsalar tsaro ne a kasar.
Asali: Legit.ng