Tinubu Ya Sa Labule da Tawagar Majalisar Shari'ar Musulunci ta Najeriya a Villa, Bayanai Sun Fito
- Bola Ahmed Tinubu ya sa labule da manyan malaman addinin musulunci a fadar gwamnati Aso Villa da ke Abuja yau Alhamis
- Wannan zama ya zo kwana biyu bayan shugaban majalisar shari'ar musulunci a Najeriya ya yi nadamar goyon bayan Muslim-Muslim
- Babu cikakken bayani kan abubuwan da za a tattauna a taron amma ana ganin tsaro da tattalin arziki ne a sahun gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na ganawa yanzu haka da mambobin majalisar koli ta shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN).
Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa taron manyan malaman musuluncin da Shugaba Tinubu na gudana yanzu haka a fadar shugaban ƙasa da ke birnin Abuja.
Wannan ganawa na zuwa ne sa'o'i 48 kacal bayan shugaban majalisar shari'a SCSN na ƙasa, Sheikh Abdur-Rasheed Hadiyyatullah, ya yi nadamar goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehin malamin ya bayyana nadamar majalisar na goyon bayan titikin Tinubu da Shettima, mabiya addini ɗaya a babban zaben shugaban ƙasa da aka yi bara.
Yayin wata hira da ƴan jarida ranar Talata a Abuja, Sheikh Hadiyyatullah, ya haifar da sabon cece-kuce kan tikitin jam’iyyar APC na Musulmi da Musulmi a zaben 2023.
Shugaban SCSN ya ƙara da bayanin cewa tikitin Muslim-Muslim da suka marawa baya, ya ba su mamaki yayin da ya gaza kai matakin da suka yi tsammani.
A cewarsa, tikitin mabiya addinin ɗaya da Shugaba Tinubu ya zaɓa har ya samu nasara a zaben da ya gabata bai kawo wani canji mai kyau ga rayuwar ‘yan Najeriya ba.
Wace ajenda za a tattauna a taron Tinubu da mambobin SCSN?
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a bayyana muhimman batutuwan da tawagar mambobin majalisar shari'a zasu tattauna da shugaban ƙasa ba.
Amma dai ana hasashen batun yanayin tattalin arziki da taɓarɓarewar tsaro ka iya zama abubuwan da za a fi maida hankali a zaman, rahoton Vanguard.
Gwamna Yahaya ya yi nasara a ƙara ɗaya
A wani rahoton kun ji cewa Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan karar da jam'iyyar ADC da ɗan takarar gwamna suka nemi tsige Gwamna Inuwa Yahaya.
A zaman sauraron karar, kotun ta yi watsi da ƙarar bayan lauyan masu kara ya janye, ta kuma sanya ranar yanke hukunci a ƙarar PDP.
Asali: Legit.ng