Tsagerun Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Matasa Uku a Jihar Arewa

Tsagerun Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Matasa Uku a Jihar Arewa

  • Wasu mahara da ake zaton ƴan bindiga ne sun sace wani basaraken ƙauye da matasa uku a jihar Kwara
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa jami'an tsaro sun cafke mutum 3 da ake zargi da hannu a harin
  • Kakakin ƴan sandan Kwara ta ce a yanzu dakarun yaƙi da masu garkuwa sun fara aikinsu kan waɗanda ake zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake da wasu matasa uku a yankin Afin da ke gundumar Ile-Ire a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, maharan sun yi awon gaba da mutanen ne ranar Talata, 16 ga watan Janairu da daddare.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji yan bindiga, sun ceto mutanen da suka sace a jihar Arewa

An yi garkuwa da basarake a Kwara.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Shugaban Al'umma da Matasa 3 a Kwara Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Sai dai rundunar ‘yan sanda ta ce jami'anta sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da basaraken da sauran matasan guda uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take tabbatar da faruwar lamarin, jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, DSP Toun Ejire-Adeyemi, ta bayyana sunan basaraken da aka sace da, Simon Ibiwoye.

Kakakin ƴan sandan ta ƙara da bayanin cewa basaraken shi ke riƙe da sarautar Olukotun na Afin, kuma an yi garkuwa da shi tare da wasu matasa uku.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

DSO Ejire-Adeyemi ta ce:

"Maharan sun tafi da mutanen zuwa inda ba a sani ba, amma rahoto na isa kunnen ƴan sanda, nan take sojoji, dakarun ƴan sanda da mafarauta suka mamaye jejin yankin.
"Garin haka ne jami'an tsaron suka yi nasarar cafke mutane uku da ake zargin sune ƴan leƙen asirin masu garkuwa da mutanen, waɗanda har yanzu ba su shiga hannu ba.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue

"An kwato wata wayar salula inda aka ga hotunan wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne domin gane su cikin sauki."

Ta kara da cewa a yanzu an miƙa waɗanda ake zargin ƴan leken asirin ne ga dakarun yaƙi da masu garkuwa na rundunar ƴan sanda a Ilorin don ɗaukar mataki na gaba.

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Ofishin Jami'an Tsaro

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun halaka mace yayin da suka kai mummunan hari ofishin jami'an tsaro ƴan banga a jihar Ebonyi ranar Talata.

Shugaban ƙaramar hukumar Ohaukwu, Mista Odono, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa wannan ba shi ne na farko ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262