Kano: Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Daurin Gidan Yari Kan Satar Babur
- Wani ɓarawon babur a jihar Kano ya girbi abin da ya shuka na laifin aikata bayan wata kotun Musulunci ta zartar maaa da hukunci
- Kotun dai ta yanke wa ɓarawon babur ɗin hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni tara bayan ta same shi da laifin sata dumu-dumu
- Wanda ake zargin dai bai wahalar da kotu ba inda ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na satar babur wanda kuɗinsa ya kai N350,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Gama PRP cikin birnin Kano, ta yanke wa wani Bashir Sani Ungoggo hukuncin watanni tara a gidan gyaran hali bisa samunsa da laifin satar babur.
An gurfanar da wanda ake zargin ne da laifin shiga ma’aikatar filaye da safiyo ta jihar Kano, tare da sace babur wanda kuɗinsa ya kai N350,000 mallakin wani Ibrahim Mansur, cewar rahoton Daily Trust.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne bayan mai gabatar da ƙara, Aliyu Abidin Murtala, ya karanta masa tuhumar da ake masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Don haka alƙalin kotun, Malam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukuncin ɗaurin watanni tara a gidan gyaran hali, sannan ya bayar da umarnin a mayar wa mai babur ɗin kayansa.
Ko a baya wata kotun shari'ar Musulunci ta zartar da hukuncin bulala 20 da zaman gidan gyaran hali na watanni shida, kan wasu mutum shida bisa laifin haɗa baki tare da ƙwace a jihar Kano, rahoton Vanguard ya tabbatar.
An gurfanar da ma'aurata a gaban kotu
Wasu ma'aurata Mista & Misis Matthew Auta mazauna ƙaramar hukumar Tudun Wada ta jihar Kano sun gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Nomansland.
Miji da matar dai sun gurfana a gaban kotun ne bisa laifin haɗa baki da sace wata yarinya ƴar shekara 17 mai suna Amira Isah Takai.
Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta zargin da ake musu na satar yarinyar a gaban kotun tare da neman a bayar da belinsu.
Kotu Ta Tura Matashi Gidan Gyaran Hali
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotun majistare da ke zamanta a jihar Kano, ta tura wani matashi gidan gyaran hali bisa zarginsa da halaka wani limamin masallaci.
Ana tuhumar dai matashin da laifin kisan kai ne bayan ya dabawa limamin wuƙa mai kaifi a bayansa, wacce ta yi sanadiyyar rasuwarsa har lahira.
Asali: Legit.ng