“Tsaraicina Na Mijina Ne Shi Kadai”: Jarumar Fim Ta Caccaki Mazan Da Ke Neman Kwanciya da Ita

“Tsaraicina Na Mijina Ne Shi Kadai”: Jarumar Fim Ta Caccaki Mazan Da Ke Neman Kwanciya da Ita

  • Uche Ogbodo ta mayar da martani ga mazan da ke damunta a soshiyal midiya saboda suna son yin soyayya da ita
  • Ta ce ta tsare kanta ga mijinta tsawon shekaru shida da suka wuce kuma bata shirya keta haddinsa ba
  • Jarumar ta kara da cewar ba za ta zama irin abokan sana'arta da ke yawon bin maza suna kwanciya da su ba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fitacciyar jarumar Nollywood, Uche Ogbodo ta yi martani ga mazan da ke damunta da sakonni a soshiyal midiya. Maza na damunta da zancen soyayya duk da cewar tana da igiyar aure a kanta.

Matar wacce ta haifi yara uku ta fada masu cewa tana da aure kuma jikinta na mijinta ne shi kadai.

Kara karanta wannan

"Na fasa kada a raba auren ina sonsa", Matar da ta maka mijinta a kotu ta yi amai ta lashe

Jarumar Nollywood ta ce jikinta na mijinta ne shi kadai
“Tsaraicina Na Mijina Ne Shi Kadai”: Jarumar Fim Ta Caccaki Mazan Da Ke Neman Kwanciya da Ita Hoto: @ucheogbodo
Asali: Instagram

Ta kara da cewar mijinta shine kadai ke ratsawa ta wajen tsawon shekaru shida da suka wuce kuma bata shirya ba wasu mazan dama a rayuwarta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogbodo ta ce ba za ta zama irin takwarorinta ba

Jarumar wacce ta haifi 'da namiji a bara ta yi bayanin cewa ya kamata su daina fada mata cewar ta zamo irin abokan sana'arta.

Ta yi bayanin cewa an la'anci duk matar da ke da aure sannan take bin maza suna kwana da ita.

A cewarta, mutanen da ke irin haka suna ja wa kansu tsinuwa ne.

Matashiyar wacce bata wasa da lamarin iyalinta ta shawarci yan mata da su daina yawon bin mazan banza sannan su zauna da namiji daya.

Kalli wallafarta a kasa:

Jama’a sun yi martani ga rubutun Uche Ogbodo

@sussannerichard:

“Dan kanfen makaryaciya ya kama da wuta.”

Kara karanta wannan

"Wani ya dauka yace ta mutu": Budurwa ta koka yayin da 'yar uwarta ta bata bayan barin makaranta

@mrs_pretty_:

“Wannan antin da karya.”

@cwalaata;

“Don kin auri yaron da ya girme maki sosai da sosai bayan kin gama yawon ta zubar. Kin san cewa ke kike jin dadin auren nan sama da kowa.”

@shilz274:

"Basu gama damun masu surar 8 ba sai masu surar W za su zo suna damu."

@queen_izzyy1:

"Mijin wannan sai tashin kanta yake yi."

Jarumar fim ta fadi dalilinta na musulunta

A wani labarin kuma, jarumar fina-finan Nollywood, Mercy Aigbe ta bayyana dalilin watsar da addinin Kirista.

Aigbe ta ce ta koma addinin Musulunci ne saboda soyayya wacce ta hada ta mijinta a yanzu, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng