Hadimin Buhari Ya Kawo Shawara da Pantami, Mutane Suka Koma Gayyar Hada Kudin Fansa
- Babban Ministan tsaro ya ce doka ba ta halattawa mutane yin gayya a tara kudin biyan fansa ba
- Muhammad Badaru Abubakar ya shaida haka bayan taron FEC da aka yi a fadar Aso Villa na makon nan
- Gwamnatin tarayya ta nuna idan aka daina bada kudi ga ‘yan bindiga, za a daina satar Bayin Allah
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Gwamnatin Najeriya ta ja kunnen al’umma a game da tattara kudin fansa ga miyagu masu yin garkuwa da mutane.
Gwamnatin tarayya ta tunawa jama’a akwai dokar da ta haramta yin gayyar hada kudin biyan fansa, The Nation ta kawo rahoton.
Idan jama’a za su daina biyan kudin fansar da aka nema, an rahoto Alhaji Badaru ya ce hakan zai kashewa ‘yan bindiga kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jiyan ne kuma Sufetan ‘yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun da Ministan Abuja, Nyesom Wike, suka dauki sabon alwashi.
IG Kayode Egbetokun ya kaddamar da dakarun SIS domin maganin ‘yan bindigan da ke dauke mutane domin karbar kudin fansa.
Isa Pantami ya nemowa 'yan bindiga N50m
Hakan yana zuwa ne bayan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya taimaka wajen samun N50m a ceto yaran Mansoor Al-Kadriya.
An ji yadda wani abokin tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin ya biya kudi da nufin kubutar da yaran da aka dauke.
..."a cafke tsohon Ministan sadarwa"
Demola Rewaju ya ce kamata ya yi hukuma ta cafke Pantami bisa zargin yunkurin kawowa tsaro barazana saboda nemo gudumuwar.
Hadimin na Atiku Abubakar ya fadi wannan a X da aka fi sani da Twitter, ya caccaki gwamnati da cewa ba ta san abin da take yi ba.
Shawarar Bashir Ahmad
Bashir Ahmaad wanda ya taba zama mai taimakon shugaban kasa, ya kawo shawarar kawo dokar kashe 'yan garkuwa da mutane.
‘Dan siyasar ya yi magana a shafin X, ya ce idan majalisa ta fito da dokar kashe ‘yan bindiga, za a samu saukin masu neman kudi da rai.
Malam Bashir ya ce yana tattaunawa da Sanata Kawu Sumaila da Ghali Tijjani Mustapha domin su kirkiro dokar a majalisun tarayya.
Jan kunnen Ministan tsaro
An ji Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya ce wannan salo da aka dauko zai kara munanan lamarin garkuwa da mutane ne.
Muhammad Badaru Abubakar ya yi wannan gargadi da yake zantawa da manema labarai bayan taron FEC da aka yi a fadar Aso Villa.
Asali: Legit.ng